Ganyen Yalo na da sinadarin potassium wanda likitan koda yace na da illa ga mai cutar koda kuma na iya tsai da zuciya a rasa rai.
Ikirari:
Akwai wani sako dake yawo a kafar tura sakwanni ta WhatsApp dake cewa;
YADDA ZA A WANKE QODA (KIDNEY) CIKIN SAUKI BA TARE DA YIN DIALYSIS A ASIBITI BA!
A nemi Ganyen Yalo🌿 wato (Garden Egg Leaves), Sai a Dan wanke ganyen da Ruwa me kyau Sai a yayyankashi🔪🌿 kanana-kanana, Sai a zuba a tukunya me kyau tare da ruwa me kyau, Sai a dora a kan wuta tsawon mintuna⏰ goma 10.
Sai a tace a saisaitashi kaman shayi🍵, idan ya Dan huce Sai a shanye cikin karamin Kofi daya🍵, Bayan an shanye da Dan wasu awowi in aka ji fitsari a yi a fili ta yadda za a ga kalar Fitsarin ya chanza tare da fitar da wasu cututtuka Daga Qoda (Kidney) Zuwa mara.”

Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi kwararren likitan koda a asibitin kasa dake Abuja Dr. Abdulshahid Sarki inda yace babu wani bincike na kimiyya daya tabbatar da wancan ikirari.
“Shi shan maganin gargajiya wanda ake amfani da ganyen yalo bashi da tushe a kimiyyance. Hasalima sai dai ya kawo matsala saboda akwai sinari na potassium da shi wannan ganyen yake kunshe dashi. Idan aka ce za’a sanya a ruwa a mutsuttsukashi to zai fitar da sinadarin na potassium wanda cewa in mutum yana da ciwon koda zai kara masa sidanarin potassium kuma Idan yayi yawa yana da Illar a jika har yana iya haddasa rasa rai domin kuwa zuciya na iya tsayawa lokaci da take aikin ta.”
Yace shan isasshen ruwa akai-akai da kuma abinci mai gina jiki shine abu mai kyau don kara lafiya da kare koda.
Akwai dai binciken masana kimiyya kan amfanin ganyen yalo wanda ya nuna cewa yana da amfani a jiki amma babu inda binciken ya nuna cewa yana wanke kodar mutum.
Sakamakon bincike:
Bisa bayanan likitan koda da kuma binciken masana kan ganyen yalo wanda ba’a sami wani waje da ya tabbatar da wancan ikirari ba ya sa kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.
Aikinku yana kyau. Allah yasa mu dace amin