BindiddigiIna Gaskiyar Cewa Citta Da Lemon Tsami Na Maganin...

Ina Gaskiyar Cewa Citta Da Lemon Tsami Na Maganin Kuraje?

-

Akwai dai magungunan gargajiya a Afrika da likitanci ya amince da su, kuma an sha yi shekaru aru-aru ana dacew, to sai dai akwai wasu da kan kasance kodai suna da illa ko kuma ba maganin abinda aka ce sunayi bane.

Batu:

Akwai wani shafin Facebook mai suna HANAFARi ya wallafa wani ikirari da hotuna a ranar 7 ga watan Janairun 2025 inda yake cewa; “Masu fama da irin wanan kurajen su markada lemon 🍋 TSAMI da citta surinka shafawa inshallahu kurajen zasu mutu.”
Hoton ikirarin dake cigaba da yaduwa

Bincike:

Kasancewar wannan batu ne daya shafi fata kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi wata kwararriyar likitar fata dake aiki a cibiyar lafiya ta kasa dake Jabi Abuja mai suna Dakta Zainab Babba Danagundi inda ta bayyanawa Alkalanci cewa a kimiyyance ba gaskiya bane domin kuwa mai makon magani ga fata hadin citta da lemon tsami illa zaiwa fata.
“Wadannan irin kuraje dake hoton da akai wannan ikirari ana iya yankesu ne ko kuma a konasu da machine, ba’a amfani da lemon tsami ko citta.”
Dakta Zainab ta kara da cewa “citta iya kawo borin jini ma fata (irritate) yayin da lemon tsami na iya haddasa matsalar fata Idan mutum ya sha fa kuma ya shiga rana (photosensitivity rash) a wasu lokuta ma sai kaga fatar mutum tayi kamar ta kone.”

Sakamakon bincike:

Bisa la’akari da bayanan kwararriyar likitar fata na matsalolin da shafa citta da lemon tsami zai iya haddasawa fata da kuma rashin sahihan alkaluma da bayanai a kimiyyance  yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wancan ikirari na citta da lemon tsami na maganin wasu kuraje iƙirarin ƙarya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar