BindiddigiIna gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa...

Ina gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa tsakanin Sudan da Chadi?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa yadda Sudan ke zargin Chadi da marawa ‘yan tawayen RSF baya, wanda ya kai Sudan ta kai karar Chadi kungiyar AU kan baiwa RSF makamai. Amurka da Faransa dai basa cikin kasashen dake rura wutar rikicin Sudan. Kuma babu wani sihihin bayani da ya nuna hakan. Ya sa Alkalanci cewa wancan ikirari na cewa Amurka da Faransa ke son haddasa yiki tsakanin Sudan da Chadi karya ne.

 

Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada jita-jita da labaran karya.
Iƙirari:
Akwai wani shafin kafar sada zumunta na TikTok mai suna @zilaihatmustafa2 (Ali Suwaga Hausa 2) ya wallafa wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna bakwai da sakan takwas a ranar 29-03-2025, inda maimagana a cikin bidiyon yake iƙirarin cewa ƙasashen Amurka da Faransa ke son haddasa yaƙi tsakanin Sudan da Chadi.
Bincike:
Taƙaddama tsakanin ƙasar Sudan da Chadi dai ta kwana biyu ana yi. Gwamnatin Sudan dama wasu jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya sun sha zargin Chadi da goyawa ƴan tawayen RSF baya.
Galibin dakarun RSF dai mutanen yankin Darfur ne wanda tun fil azal  al’umomin yankin Darfur ƴan uwan juna ne da makwabtansu da ke gabashin Chadi.
Gwamnatin Sudan ta daɗe tana gargaɗin gwamnatin Chadi da ta daina taimakawa mayaƙan RSF, ƙasar ta Chadi ta musanta.
A kwanakin baya ma dai wani babban jami’in gwamnatin Sudan ya yi barazanar kai wa Chadi hari a cewar sa idan har “ba ta daina tallafawa abokan gaban Sudan ba wato RSF.”
A ɓangaren Chadi kuwa wani babban sojan ƙasar Birgediya Janar Acheikh Issakha Acheikh ya bayyana shirin dakarun ƙasar na kare ta, kuma ya sha alwashin kai wa Sudan martani da ya dace na hare-hare.
A Nuwanban shekarar 2024 sai da ministan  Shari’ar kasar ta Sudan Muawiya Osman ya ce gwamnatin Burhan ta kai karar kasar Chadi gaban kungiyar Tarayyar Afirka.
Da yake magana da manema labarai, ciki har da AFP, Osman ya ce gwamnati ta buƙaci a biya ta diyya, ya kuma zargi Chadi da “sayar da makamai ga mayakan ‘yan tawaye” da kuma “illata ‘yan kasar Sudan”.
Tuni dai sojojin ƙasar ta Sudan suka kwace babban birnin ƙasar Khartoum da wasu garuruwa dake kewaye daga hannun mayaƙan RSF.
Sakamakon binciken:
Bisa la’akari da alaƙar da takun sakar dake tsakanin shugabannin Sudan da na Chadi kan batun zargin taimakawa ƴan tawayen RSF, dama kai karar Chadi zuwa Kungiyar Tarayyar Afrika AU, da kuma samun musayar yawu tsakanin ƙasashen biyu yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa Amurka da Faransa na da hannu ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar