Hukunci: Ƙarya ne
Bisa yadda Sudan ke zargin Chadi da marawa ‘yan tawayen RSF baya, wanda ya kai Sudan ta kai karar Chadi kungiyar AU kan baiwa RSF makamai. Amurka da Faransa dai basa cikin kasashen dake rura wutar rikicin Sudan. Kuma babu wani sihihin bayani da ya nuna hakan. Ya sa Alkalanci cewa wancan ikirari na cewa Amurka da Faransa ke son haddasa yiki tsakanin Sudan da Chadi karya ne.
Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada jita-jita da labaran karya.
Iƙirari:
Akwai wani shafin kafar sada zumunta na TikTok mai suna @zilaihatmustafa2 (Ali Suwaga Hausa 2) ya wallafa wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna bakwai da sakan takwas a ranar 29-03-2025, inda maimagana a cikin bidiyon yake iƙirarin cewa ƙasashen Amurka da Faransa ke son haddasa yaƙi tsakanin Sudan da Chadi.
Bincike:
Taƙaddama tsakanin ƙasar Sudan da Chadi dai ta kwana biyu ana yi. Gwamnatin Sudan dama wasu jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya sun sha zargin Chadi da goyawa ƴan tawayen RSF baya.
Galibin dakarun RSF dai mutanen yankin Darfur ne wanda tun fil azal al’umomin yankin Darfur ƴan uwan juna ne da makwabtansu da ke gabashin Chadi.
Gwamnatin Sudan ta daɗe tana gargaɗin gwamnatin Chadi da ta daina taimakawa mayaƙan RSF, ƙasar ta Chadi ta musanta.
A kwanakin baya ma dai wani babban jami’in gwamnatin Sudan ya yi barazanar kai wa Chadi hari a cewar sa idan har “ba ta daina tallafawa abokan gaban Sudan ba wato RSF.”
A ɓangaren Chadi kuwa wani babban sojan ƙasar Birgediya Janar Acheikh Issakha Acheikh ya bayyana shirin dakarun ƙasar na kare ta, kuma ya sha alwashin kai wa Sudan martani da ya dace na hare-hare.
A Nuwanban shekarar 2024 sai da ministan Shari’ar kasar ta Sudan Muawiya Osman ya ce gwamnatin Burhan ta kai karar kasar Chadi gaban kungiyar Tarayyar Afirka.
Da yake magana da manema labarai, ciki har da AFP, Osman ya ce gwamnati ta buƙaci a biya ta diyya, ya kuma zargi Chadi da “sayar da makamai ga mayakan ‘yan tawaye” da kuma “illata ‘yan kasar Sudan”.
Da yake magana da manema labarai, ciki har da AFP, Osman ya ce gwamnati ta buƙaci a biya ta diyya, ya kuma zargi Chadi da “sayar da makamai ga mayakan ‘yan tawaye” da kuma “illata ‘yan kasar Sudan”.
Tuni dai sojojin ƙasar ta Sudan suka kwace babban birnin ƙasar Khartoum da wasu garuruwa dake kewaye daga hannun mayaƙan RSF.
Sakamakon binciken:
Bisa la’akari da alaƙar da takun sakar dake tsakanin shugabannin Sudan da na Chadi kan batun zargin taimakawa ƴan tawayen RSF, dama kai karar Chadi zuwa Kungiyar Tarayyar Afrika AU, da kuma samun musayar yawu tsakanin ƙasashen biyu yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa Amurka da Faransa na da hannu ƙarya ne.