BindiddigiHotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la’akari yadda VOA ta taba wallafa hotunan a Disembar  shekarar 2021 lokacin da mataimakin gwamnan ya je yiwa Kwankwaso ta'aziyya.Sannan tabbacin da aka samu daga jami’in gwamnati, Alkalanci ta tabbatar da cewa ikirarin cewa waɗannan hotuna na Nasiru Yusuf Gawuna da Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin sababbi ƙarya ne.
Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna a shafukan sada zumunta na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tare da Nasiru Yusuf Gawuna.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Dan Almajiri ya wallafa wannan Iƙirarin cewa Sanata Kwankwaso ya kira Nasiru Yusuf Gawuna gidansa inda suka gana.
Hoton Iƙirarin karya dake yaduwa
Haka shima wani shafin  mai suna Lamara Saraki shima ya wallafa wadannan hotuna da Iƙirari.
Hoton Iƙirarin karya dake yaduwa
Masu yaɗa hotunan suna ta iƙirarin cewa “Kwankwaso ya kira Gawuna gidansa,” suna mai nuna cewa hotunan sababbi ne na wata ganawa da aka yi kwanan nan.
Bincike: 
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike don gano sahihancin hotunan da kuma lokacin da aka ɗauke su.
Da Alkalanci ta sanya hoton a Google lens sai sakamakon ya nuna cewa kafar yada labarai ta Muryar Amurka VOA ta wallafa hotunan tun ranar 23 ga watan Disembar 2021.
Wani shafin na Facebook ma mai suna Hon. Kamilu Aminu ya wallafa ranar ta 23 ga watan Disamba, 2021.
Wata hujjar da ke tabbatar da hakan ita ce yanayin hotunan, wanda ya yi daidai da zamanin ɓarkewar cutar Corona (COVID-19), inda ake iya ganin takunkumi fuska da aka yi amfani da su a wancan lokacin.
Don samun ƙarin haske, Alkalanci ta tuntuɓi Abdullahi Amir Kuma, wanda yana ɗaya daga cikin masu kula da harkokin midiya na gwamnatin Kano. Ya tabbatar wa Alkalanci cewa lallai waɗannan hotuna tsofaffi ne da aka yi a wancan lokaci.
Sakamakon Bincike: 
Bisa la’akari yadda VOA ta taba wallafa hotunan a Disembar  shekarar 2021 lokacin da mataimakin gwamnan ya je yiwa Kwankwaso ta’aziyya.Sannan tabbacin da aka samu daga jami’in gwamnati, Alkalanci ta tabbatar da cewa ikirarin cewa waɗannan hotuna na Nasiru Yusuf Gawuna da Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin sababbi ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai babban birnin ƙasar Nijar, shugaban...

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Karanta wannan

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da...

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar