Hukunci: Ƙarya ne
Bisa bayanin hukumar EFCC a Kano da Abuja da suka fadawa Alkalanci cewa hoton da labarin ba daga gere su bane, sannan matashin da aka saka hoton sa ya ƙaryata labarin wanda yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin cewa EFCC ta kama matashin da aka sanya hoton sa cewa ya canza asusun bankin masallaci da na shi ƙarya ne.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa wani labari ɗauke da hoton wani matashi inda yayi iƙirarin cewa hukumar EFCC tayi holen wani matashi bisa samun shin da laifin canza asusun bankin masallaci da nashi asusun.
“EFCC Ta Cafke Wani Matashi Bisa Zargin Sauya Asusun Masallaci Da Nasa Domin Karɓar Tallafi Kai Tsaye.”


Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba wannan hoton a shafin hukumar EFCC inda a nan take wallafa hotunan duk wanda ta kama kuma tayi holen sa, amma babu hoto ko wannan labarin wannan matshin.
Sannan Alkalanci ta tuntuɓi hukumar EFCC dake Kano inda ta bayyanawa Alkalanci cewa wannan hoton da labarin wannan matashi ba daga EFCC take ba.
Sannan Alkalanci ta tuntuɓi shalkwatar hukumar ta EFCC Abuja inda suka bayyana cewa wannan labari ba daga gare su bane.
Haka zalika Alkalanci ta gano wata hira da matakin dake hoton yayi da gidan rediyo na Freedom inda ya ce shi ba a kama shi ba kuma bai aikata abinda aka faɗa ba.
Sakamakon bincike:
Bisa bayanin hukumar EFCC a Kano da Abuja da suka bayyana wa Alkalanci cewa hoton da labarin ba daga gere su bane, sannan matashin da aka saka hoton sa ya ƙaryata labarin wanda yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin cewa EFCC ta kama matashin da aka sanya hoton sa cewa ya canza asusun bankin masallaci da na shi ƙarya ne.
