Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun shafukan da suka fara wallafa hoton sun bayyana shi a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI, da kuma rashin samun daidaito na hoton kan shekarun Zohran Mamdami lokacin da ake iƙirarin an ɗauki hoto tare da bincike da manyan gidajen jaridu irinsi BBC, Washington Post da France24 daya bayyana hoton a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa Mamdami bashi da alaƙa da file ɗin Epstein da ake yaɗawa.
Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya.
Iƙirari:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Alhassan Mai Lafiya daya wallafa wani hoto dake iƙirarin cewa akwai magajin garin New York Zohran Mamdami a cikin file ɗin inda yayi rubutu kamar haka;
“An bankaɗo sirrin magajin garin New York (Zohran Mamdani) da mahaifiyarsa acikin file ɗin lalata na Epstein.”

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa hoton an fara yaɗa shi a wasu shafukan X da harshen Turanci wanda aka rubuta cewa hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.

Wannan iƙirari ya samo asalin bayan billar sakon email na shekarar 2009 wanda a ciki akwai sunan Bill Clinton, Jeff Bezos da Mira Nair mahaifiyar Zohran Mamdami.

Alkalanci ta sanya hoton da ake yaɗawa a manhajar gano hotunan AI na Google inda sakamako ya nuna cewa an haɗa hoton ne ta amfani da ƙirƙirarriyar basirar AI.

Haka zalika Alkalanci idan za ayi amfani da shekarun Zohran Mamdami ya zama cewa a shekarar 2009 shekarun sa 18 kenan wanda ya ci karo da abinda ake son nunawa a hoton.
Sannan duba da yadda aka ɗauki hoton akwai yanayi na da zaiyi wuya hakan ta faru.

Alkalanci ta gano cewa manyan gidajen jaridu irin su Washington Post, France24, BBC duk sun tantance hoton tare da bayyana shi a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI.
Sakamakon bincike: