BindiddigiHoto haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI kan yaƙin Sudan

Hoto haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI kan yaƙin Sudan

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa manyan alamomin da suka tabbatar da hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne, shafin da ya fara wallafa bidiyon da aka ɗakko hoton ya ayyana bidiyon a matsayin haɗin AI, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton na ƙarya ne.
Yayin da ƙasashen duniya da mutane ke cigaba da magana tare da Allah wadai da abubuwan dake faruwa a Sudan.
A duk lokutan wani rikici ko yaƙi hotuna da bidiyon haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI na yaɗuwa domin cimma wata manufa.
Duk da cewa kashe-kashen ko ta’asa na faruwa.
Iƙirari:
Wasu shafukan sada zumunta a Sudan dama waɗanda ke magana da harshen Hausa sun yaɗa wani hotu da ake iƙirarin cewa bayan an ƙona gidan ta ita da yaranta suna jiran mutuwar su.
Wata mata ce da Ƴan tawayen Sudan suka jefa a cikin wani kwazazzabo, tana rungume da ɗanta a kirjinta, tana jiran ajalin ta bayan sun ƙone gidanta akan idonta!!
Wannan hoto ba wani shiri ne daga labarin Ashabul Ukhdud ba, wannan hoton daga Sudan ne mai jinya da raɗaɗi, Sudan da aka manta da ita, Sudan da hawaye suka ƙafe, Sudan da duniya bata damu da ita ko ɗan kaɗan ba!!
Hoton Hadin AI dake cigaba da yaduwa
Shima wannan shafin facebook ya wallafa wannan hoto tare da dogon rubutu.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta ga no cewa wannan hoto da ake cigaba da yaɗawa haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
A hoton dai akwai alamomi da dama dake tabbatar da hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI misali, inuwar wasu dake tsaye. Sannan shafin Tiktok da shine farko da ya wallafa bidiyon da aka dakko hoton mai suna @khoubaib.bz ya ayyana bidiyon a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI.
Alkalanci ta tabbatar da wasu bidiyon kashe-kashe da dakarun RSF sukayi a el-fasher to amma wancan hoto dai ba na gaskiya bane.
Sakamakon bincike:
Bisa manyan alamomin da suka tabbatar da hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne, shafin da ya fara wallafa bidiyon da aka ɗakko hoton ya ayyana bidiyon a matsayin haɗin AI, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton na ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar