Fayyace abubuwaHanyoyin kare kai daga faɗawa hannun masu zambar ɗaukar...

Hanyoyin kare kai daga faɗawa hannun masu zambar ɗaukar aiki

-

Gane bambanci tsakanin sihihan guraben aikin da na bogi yana iya zama abu mai wahala, wanda hakan na iya janyo asarar lokaci, kuɗi, da bayanan sirri ga masu neman aiki.

A shekarar 2023, bisa ga rahoton Identity Theft Resource Center, yaudarar neman aiki ta karu da kashi 118% fiye da shekarar da ta gabata.
Нака kuma, ayyukan bogi sun zama babban ƙalubale ga masu neman aiki — inda kashi 81% na masu ɗaukar ma’aikata suka amince cewa kamfanoninsu sun taɓa saka irin waɗannan ayyuka.
Don kare bayanan sirrinka, kuɗin ka, da lokacin ka yayin neman aiki, ga alamomin ayyukan bogi tare da hanyoyin guje wa faɗawa tarkon masu zamba.
Kamfanoni ko hanyoyin sadarwa na bogi
masu zambatar mutane sukan ƙirƙiri shafukan yanar gizo, adireshin imel, lambobin waya, da shafukan sada zumunta na ƙarya don su bayyana kamar cewa na gaske ne .
Suna iya turo maka da mahada (links) ko files masu haɗari don su saci bayananka ko su saka ƙwayar cutar kwamfuta wato(virus) a na’urarka.
Idan aka turo maka da link, ka kwafi ka sanya a sabon shafi don tabbatar da ingancin sa .
Shafuka na gaskiya da tsaro suna farawa ne da “https”.
Don haka sai an lura da ƙananan bambance-bambance a adireshin da aka yi don ruɗar da mutane.
Idan dole ne sai ka buɗe files kamar takadar neman aiki daga wani wanda ba ka sani ba, idan zaka iya duba shi ba tare da ka sauke shi ba. Misali, Google yana baka damar duba file a sabon shafi kafin ka sauke shi.
Haka kuma, zaka iya tura file din zuwa USB flash drive ka bude shi a wata na’ura da ba a haɗe take da intanet — wannan yana hana masu kutse su gane ka buɗe bayanan ba .
Ku tabbata kwamfutarku tana da sabuwar sigar tsaro (macOS ko Windows) Wannan zai tabbatar cewa kwamfutarku tana gane ƙwayoyin cuta (virus) da aka sani kuma tana tsayar da su kafin su yi barna. Domin ƙarin kariya, yi amfani da manhajar kariya daga ƙwayoyin cuta wato(antivirus software).
Kura-kurai na rubutu ko yadda ake tsara kalmomi da jimloli yadda ya dace
Masu zamba sau da yawa sukan yi kurakurai da gangan a rubuce don su guje wa tsarin tsaro da ke toshe saƙwannin zamba. Wani lokaci kuma saboda fassarar kai tsaye daga wani harshe ce, ko kuma hanyar gane masu rauni da za su yarda da zamba.
Kamfanonin gaskiya suna bin ƙa’idar ƙwararru (professionalism), don haka idan kuka ga rubutu cike da kura-kurai to ku yi hattara.
Kamfani yana neman bayanan sirri da wuri
Wasu masu zamba sukan ƙirƙiri aikin bogi don tara bayanan mutum da za su yi amfani da su wajen satar asali ko damfara.
Ka kula da lokacin da ake tambayar ka bayanai da kuma irin bayanan da ake nema.
Ka tabbatar da gaskiyar kamfanin ko ma’aikatar kafin ka ba su bayananka. Wasu ma suna iya ƙirƙirar kwamiti na bogi don su rinjaye ka ka yarda da su.
Ana neman kuɗi ko canza kuɗi ta hanyar damfara
Idan wani kamfani yana roƙonka ka biya wani abu kamar kayan aiki, ko canja kuɗi ta asusunka don wani ƙarin albashi to wannan zamba ce.
Kamfani na gaskiya ba zai taba neman kudi daga mai neman aiki ba.
Turo maka tayin aiki ba tare da ka nema ba
Wasu masu zamba sukan aiko maka da tayin aiki ko damar aikin da ba ka nema ba.
Ka yi taka-tsantsan da irin wadannan saƙwannin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar