A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa daga NNPC zuwa APC wanda hakan ya sa wasu ke bayyana cewa akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan da tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.
Iƙirari:
Shafin ‘Rariya Online’ ya wallafa wani labari a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 31 ga watan Disamba na shekarar 2025, inda ya yi iƙirarin cewa: “YANZU-YANZU: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya Kori Ɗan Kwankwaso Daga Muƙamin Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano Daga Muƙamin sa“.
Wannan labari ya biyo bayan jita-jitar tashin ƙurar siyasa da ake raɗe-raɗin ta kunno kai tsakanin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da mai gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda hakan ya bai wa shafuka daban-daban damar ƙirƙira da kuma yaɗa labaran ƙarya.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike don gano gaskiyar lamarin.
A yayin binciken, Alkalanci ta samu zarafin tattaunawa da Amir Abdullahi Kima, wanda shi ne Babban Mai Daukar Rahoto na Musamman kan Ma’aikatar Shari’a ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba K. Yusuf.
A hirarsa da Alkalanci, Amir Kima ya bayyana cewa: “Wannan labarin ba gaskiya ba ne. Gwamna bai sallami Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar ba.”
Sannan Alkalanci ta duba sahihan gidajen jaridu amma bata sami labarin korar dan gidan Kwankwaso ba.
Alkalanci ta ƙara da duba shafin mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin labarai amma babu wata sanarwa makamanciyar hakan. Sannan babu wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamntin jihar Kano na korar kwamishina.
Sakamakon Bincike:
Bisa ga bayanan da aka samu daga majiyoyi na kusa da gwamnati, da kuma rashin wata sanarwa a hukumance daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha ko kakakin gwamna, Alkalanci ta tabbatar da cewa labarin korar Mustapha Kwankwaso ƙarya ne da aka ƙirƙira.
