Sanata Akpabio ya sharara karya kan babu barazanar ta’addanci a Najeriya.
Shekaru sama da goma kenan Najeriya ke fama da matsalar ‘yan kungiyar Boko Haram da ISWAP da aka ayyana a matsayin kungiyoyin ta’addanci.
Batu:
Yayin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yaje gabatar da kasafin kudin shekarar 2025, shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio yayi ikirarin cewa a halin yanzu babu wani gari a Najeriya dake fuskanta barazanar ta’addanci.
kafar yada labarai ta BBC Hausa ma ta rawaito wannan ikirari.

Bincike:
A dai-dai lokacin da shugaban majalisar dattawan ke wannan ikirari akwai labarin daya fito na nuna yadda ‘yan kungiyar Boko haram suka kai hari tare da rusa gidajen da gwamnati ta gina a kauyen Dalwa mai nisan kilomita goma daga Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar litinin din data gabata wato kwana daya kafin wannan ikirari na Sanata Akpabio.
Haka zalika a ranar talata 17 ga watan Disamba an sami hatsaniya tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga biyu a Katsina wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindigar.
A tsakanin karshen watan Nuwamba da farko watan nan na Disemba ma dai an sami tashin bama-bamai sau uku a hanya da kuma wasu garuruwa a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara. Wanna harin bamai-bamai dai jami’an tsaro sun tabbatar da aukuwar su.
Kafar bindiddigi ta kuma samo ayyukan soji na yaki da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a sassan Najeriya cikin kasa da sati guda kafin sanata Akpabio yayi wannan ikirari.
A ranar 12 ga watan Desambar 2024 mai magana da yawun rundunar hadin gwiwar yaki a arewa maso yammacin Najeriya (Operation Fansan Yamma) laftanal Kanal Abubakar Abdulahi ya fitar da takardar manema labarai inda yace sojojin sun sami nasarar kashe yan fashin daji biyu tare da kwace bindugu da harsasai a jihar Zamfara.
Haka zalika a rana 11 ga watan Disemba ce sojoji suka dakile harin yan bindiga a kudancin jihar Taraba.
Rahoton kididdiga da alkaluman hukumar NBS ta Najeriya data fitar ranar litinin ya nuna yadda ake kashe mutane sama da dubu dari shida a hare-haren ta’addanci a sassan Najeriya cikin shekara guda. Yayin da rahoton ya nuna cewa anyi garkuwa da mutane sama da miliyan biyu.
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da rahotannin hare-haren yan bindiga dama kungiyoyin da aka ayyana a matsayin na ‘yan ta’adda a sassan Najeriya da kuma rashin samo sahihin bayani daga rundunonin tsaron Najeriya kan kawo karshen barazanar ta’addanci a sassan Najeriya, kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa ikirarin na shugaban majalisar dattawan Najeriya sanata Godswill Akpabio karya ne.