Fayyace abubuwaCBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

-

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin da suka amince da wani kamfanin kasuwancin kiripto mai suna Crypto Bridge Exchange Smart-Treasures wanda aka fi sani da CBEX.

Kamfanin dai yayi batan dabo ko ace ya arce duk da alkawarin daya yiwa wadanda suka sanya kudi ko hannun jari na samun kashi dari bisa dari na abinda suka sanya, wannan batan dabo ya sanya koke-koke daga ‘yan Najeriya.

Matasa da dama sun riki kasuwancin Crypto hannu bi biyu wanda hakan ke nufin akwai bukatar yin taka tsantsan wajen zuba hannun jari. 

Tuni dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta tabbatar da wannan batan dabo tare da cewa ta fara bincike.

To sai dai hukumar kula da zuba hannun jari da kamfanoni ta SEC ta ce kamfanin na CBEX ba shi da rijistar gudanar da kasuwanci zuba hannun jari a Najeriya.

Shugaban hukumar SEC Emomotimi Agama ya ce “ Idan kamfani baida rijista na nufin haramtacce ne. Don haka CBEX da bai da rijista to haramtaccen kamfani ne. 

Bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar ilimantar da mutane kan yadda zasu gane idan kamfani na da rijistar yin kasuwancin zuba jari ko kuwa?

6E54C558-43D3-4615-B21B-EB29012A6D9E.png

Hoton shafin hukumar SEC don nuna yadda zaku duba kamfanoni masu rijista SEC CSMOS 

40AF31BD-C1FC-4B5E-AD6E-BAC270936E69.png

Hoton shafin SEC CMOS dake nuna inda zaku binciki sunayen kamfanoni

BDC5C3CA-C780-4834-97B5-C122A5229392.png

Hoton shafin SEC CMOS dake nuna sakamakon binciken sunayen kamfanoni ta amfani da rubutun “First Ban”.

Hukumar SEC ita ce ke lura da kasuwar zuba hannun jari na Najeriya, sun samar da wani sashe na tantance halastattun kamfanoni mai suna SEC CMOS (capital market operator search) kuma tantance kamfanoni halastattu masu rijista kyauta ne. 

Hanyoyin da zaku gano kamfani na da rijista da SEC

1. Ziyarci shafin  SEC:
Duba  https://sec.gov.ng
2. Duba Kudin bayanai wato Database:
•  A saman shafin zaku dannan “Research Area.”
• A kasan Menu din kuje ku zabi “Database.”
• Sannan ku dannan  “Registered Capital Market Operators.”
3. Sannan sai ku je shafin CMOS :
Za’a kaiku zuwa wannan shafin: https://sec.gov.ng/cmos/#
4. Ku yi search din kamfanin da Kike bukata:
• Use the search bar provided on the page.
• Ku rubuta sunan kamfanin da kuke son tabbatar da rijistar sa yadda yake.
5. Ku duba sakamakon binciken ku:
• Idan sunan kamfanin ya fito a bangaren bincike ko muce search hakan na nufin kamfanin na da rijista da SEC.
• To amma Idan bai fito ba hakan na nufin baida rijista kuma haramtaccen kasuwanci kamfanin yake.

Ku tabbata kun tantance tare da tabbatar da cewa kamfanin zuba hannun jari na da rijista da SEC kafin ku sanya kudin ku.

Duk kamfanin zuba jari da baida rijista da SEC kamar CBEX  na iya rufewa ko guduwa a kowanne lokaci wanda zai sa wadanda suka zuba hannun jari tashi ba ko sisi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya. Iƙirari: Akwai...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna...

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai babban birnin ƙasar Nijar, shugaban...

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Karanta wannan

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar