Iƙirari:
A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda ke nuna Alhaji Ali Baba Fagge, tsohon mai ba wa gwamna shawara kan harkokin addini a gwamnatin tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
A cikin bidiyon, ana jin muryar ɗan siyasan yana furta wasu kalamai inda aka sanya hoton matar tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, kuma aka rubuta cewa “Ali Baba yabar APC…” a cikin bidiyon mai tsawan sakan ashirin da tara, anji yana cewa; “Billahillazi la’ilaha illahuwa na dauke ki munyi wata shida dake, ke daduro na ce, ke karuwa ta ce, ni mai cin amana ne, kuma fasiki ne, kuma makaryaci da tumasanci...
Wannan bidiyo ya bayyana ne kwanaki kaɗan bayan Ali Baba Fagge ya yi wata tattaunawa ta siyasa da gidan radiyo na Express, lamarin da ya jawo cece-kuce.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike na musamman kan wannan bidiyo.
Da farko, Alkalanci ta samo asalin hirar da Alhaji Ali Baba Fagge ya yi da gidan Radiyon Express a makon da ya gabata. Binciken ya tabbatar da cewa duk da ya yi martani irin na siyasa, babu inda ya furta wadancan kalamai na sabon bidiyon.
Na biyu, ta hanyar amfani da fasahar gano bidiyo da hotuna hadin AI mai suna AI Video Detector sakamakon ya bayyanawa Alkalanci cewa bidiyon da ke yawo a TikTok haɗin AI ne (Deepfake).
Sannan Alkalanvi ta fahimci masu yaɗa labarin sun yi amfani da fasahar kwaikwayon murya da motsin baki (lip-sync technology) don sanya ɗan siyasan faɗar abin da bai furta ba kuma alamu sun nuna cewa sun yayyanke asalin maganar.
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da cewa bidiyon na ɗauke da alamun sarrafa na’ura (AI), da kuma rashin gaskiyar kalaman idan aka kwatanta da asalin hirar, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan bidiyon ƙarya ne da aka ƙirƙira.
