BindiddigiBincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la’akari da cewa bidiyon na ɗauke da alamun sarrafa na’ura (AI), da kuma rashin gaskiyar kalaman idan aka kwatanta da asalin hirar, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan bidiyon ƙarya ne da aka ƙirƙira.


Iƙirari:

A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda ke nuna Alhaji Ali Baba Fagge, tsohon mai ba wa gwamna shawara kan harkokin addini a gwamnatin tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

A cikin bidiyon, ana jin muryar ɗan siyasan yana furta wasu kalamai  inda aka sanya hoton matar tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, kuma aka rubuta cewa “Ali Baba yabar APC…” a cikin bidiyon mai tsawan sakan ashirin da tara, anji yana cewa; “Billahillazi la’ilaha illahuwa na dauke ki munyi wata shida dake, ke daduro na ce, ke karuwa ta ce, ni mai cin amana ne, kuma fasiki ne, kuma makaryaci da tumasanci...

Wannan bidiyo ya bayyana ne kwanaki kaɗan bayan  Ali Baba Fagge ya yi wata tattaunawa ta siyasa da gidan radiyo na Express, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike na musamman kan wannan bidiyo.

Da farko, Alkalanci ta samo asalin hirar da Alhaji Ali Baba Fagge ya yi da gidan Radiyon Express a makon da ya gabata. Binciken ya tabbatar da cewa duk da ya yi martani irin na siyasa, babu inda ya furta wadancan kalamai na sabon bidiyon.

Na biyu, ta hanyar amfani da fasahar gano bidiyo da hotuna hadin AI mai suna AI Video Detector sakamakon ya bayyanawa Alkalanci cewa bidiyon da ke yawo a TikTok haɗin AI ne (Deepfake).

Sannan Alkalanvi ta fahimci masu yaɗa labarin sun yi amfani da fasahar kwaikwayon murya da motsin baki (lip-sync technology) don sanya ɗan siyasan faɗar abin da bai furta ba kuma alamu sun nuna cewa sun yayyanke asalin maganar.

Sakamakon Bincike:

Bisa la’akari da cewa bidiyon na ɗauke da alamun sarrafa na’ura (AI), da kuma rashin gaskiyar kalaman idan aka kwatanta da asalin hirar, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan bidiyon ƙarya ne da aka ƙirƙira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Wasu shafukan da suka dinga yaɗa ƙage da labaran ƙarya a shekarar 2025

Shekarar 2025 dai ta kasance shekarar da aka sami wasu shafukan sada zumunta da kaso mafi yawa na abubuwan...

Gaskiyar abin da ke tattare da yarjejeniyar hukumar FIRS ta Najeriya da Faransa

Biyo bayan sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar haraji tsakanin Najeriya da Faransa a wannan watan na Disamba, an yi...

Ƙarya ne: Nasiru El-Hikaya baya cikin waɗanda VOA suka kora a shekarar 2018

Akwai wani shafin Facebook mai suna Gimbiyar Hausa ya wallafa wani iƙirari kan cewa ta kori wani ɗan jaridar...

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Karanta wannan

Wasu shafukan da suka dinga yaɗa ƙage da labaran ƙarya a shekarar 2025

Shekarar 2025 dai ta kasance shekarar da aka sami...

Gaskiyar abin da ke tattare da yarjejeniyar hukumar FIRS ta Najeriya da Faransa

Biyo bayan sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar haraji tsakanin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar