Hukunci: Ƙarya ne
Bisa rashin daidaito na bidiyon da ake yaɗawa, da kuma sakamakon bincike manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI, tare da kasa samun wani hoto ko bidiyo na Kanu a gidan yarin Sokoto yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyo da ake yaɗawa na Nnamdi Kanu a Sokoto hadin AI ne.
Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta’addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bada shi ga jami’an gidajen gyara hali inda suka tasa ƙeyarsa zuwa Sokoto.
Iƙirari:
A yayin da ake ta cece-kuce kan wannan hukunci da kuma dalilin tura shi Sokoto da akayi, sai wasu shafukan sada zumunta suka dinga yaɗa hotuna da bidiyon Kanu a gidan yarin Sokoto sanye da kayan gidan yari.
Misali wani shafin Facebook mai suna Man Sagir Dan Jarida ya yaɗa bidiyon dake nuna Kanu a gidan yarin na Sokoto. Anan kuma a cikin ɗaki da abinci a gabansa duka dai yana magana da Hausa.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta kalli bidiyon da kyau tare da ganin yadda ya saka abu a bakinsa babu alamun tauna kuma babu alamun wani abu a bakin sa.
Sannan babu alamomin fuska da suke na Nnamdi Kanu ne duk da cewa akwai ƴan kamanni.
Sannan bai ɗauki komai daga kwanon dake hannun sa ba amma an ga ya ajiye abu.
Haka zalika Alkalanci ta sanya bidiyon da hotunan bidiyon a manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI inda sakamako ya nuna tabbacin cewa bidiyon haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
Babu dai wani hoto a hukumance ko wanda sahihan gidajen jaridu suka samu na Kanu a gidan yarin Sokoto.
An dai rawaito cewa wani gwamna daga kudu maso gabas ya ziyarci Kanu a Sokoto amma ba a fito da wani hoto dake nuna Kanu ba.
Sakamakon bincike:
Bisa rashin daidaito na bidiyon da ake yaɗawa, da kuma sakamakon bincike manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI, tare da kasa samun wani hoto ko bidiyo na Kanu a gidan yarin Sokoto yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyo da ake yaɗawa na Nnamdi Kanu a Sokoto hadin AI ne.
