Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun tabbacin cewa bidiyon da ake yaɗawa tsohon bidiyo ne kuma ɗan sanda da yayi holen wadanda ke bidiyon mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina ne ba Kano ba, sannab mai magana da yawun yan sandan Kano bai wallafa hoto ko bidiyon wadanda ake zargi ba duk da a wallafa tabbacin kama su, hakan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyon na yaudarar mutane ne.
Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai a jihar Kano.
Iƙirari:
Wani shafin Tiktok mai suna kafafocmero ya wallafa wani bidiyo da ƴan sanda ke holen wasu da sukai kisan kai inda suke faɗin yadda sukayi kisan. Inda aka sanya hoton mutane bakwai ƴan gida ɗaya da aka kashe a Kano tare da rubutun dake nuna cewa waɗanda sukai kisan ne.
Bidiyon ya sami mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da suka kalla.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa wannan bidiyo dake yawo akwai wani shafin Tiktok mai suna contentment9 daya wallafa shi a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2025 wato bara kenan.
Bidiyon ya sami mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar da suka kalla. Duk da cewa a hakan ma tsohon bidiyo ne ba a wannan lokaci akayi holen su ba.
Ɗan sanda dake holen masu laifin a bidiyon dai Alkalanci ta tabbatar da sunan sa Gambo Isa kuma yana aiki ne a rundunar ƴan sanda dake Katsina ba Kano ba.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa inda ya wallafa cewa rundunar ta kama mutum uku da ake zargin da kisan.
Wasu gidajen jaridu da shafukan sada zumunta dai a Kano sun wallafa hotuna da sunayen mutanen da ake zargin da kisan mutanen bakwai ƴan gida ɗaya a jihar Kano.
Sakamakon bincike: