BindiddigiBidiyon ɓera a ɗakin yaɗa shirye-shirye na Aljazeera haɗin...

Bidiyon ɓera a ɗakin yaɗa shirye-shirye na Aljazeera haɗin AI ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
La’akari da cewa wasu kafafen tantance labarai sun tabbatar da bidiyon na AI ne, tare da irin lurar da Alkalanci tayi na yadda ta zauna ba tare da ta juyo da kurar ba, da kuma yanayin sautin muryar ya tabbatar da cewa bidiyon hadin AI ne.

Akwai wani bidiyo dake yaɗuwa matuka a kafafen sada zumunta, inda ake nuna cewa ɓera ya firgita mai gabatar da labarai a ɗakin watsa labarai na gidan Talabijin na Aljazeera.

Iƙirari:

Wani shafin facebook mai suna Abdulmumin Abubakar Tsanyawa ya wallafa bidiyon inda ya rubuta; “ Bera cikin studion Aljazira  ”

Wannan bidiyo dai ya yaɗu matuka a gurare da dama kamar nan.

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa gidan jarida na newsbuzz247 ya tantance wannan bidiyo tare da yanke hukuncin cewa haɗin AI ne.

Haka zalika wata kafar jarida dake aikin tantance labarai a ƙasar indiya mai suna LatestLY  itama ta tantance wannan labara tare da yanke hukuncin cewa haɗin AI ne.

Duk da wannan bayanai Alkalanci ta kalli bidiyon da kyau inda akwai gurare dake nuna cewa bidiyon haɗashi akayi. Na farko muryar alamun anyi amfani da AI akanta, haka zalika bayan da mai gabatarwar ta tashi tsaye kujerar ta juya baya amma sai aka ga ta dawo ta zauna ba tare da ta juyo da kujerar ba. Sannan tsayar da bidiyon domin duba beran ya nuna cewa ba kamar yadda idan beran gaskiya bane.

Sakamakon bincike:

La’akari da cewa wasu kafafen tantance labarai sun tabbatar da bidiyon na AI ne, tare da irin lurar da Alkalanci tayi na yadda ta zauna ba tare da ta juyo da kurar ba, da kuma yanayin sautin muryar ya tabbatar da cewa bidiyon hadin AI ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar