Hukunci: Ƙarya ne
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano tambarin yan sandan Ghana, da kuma lambar kira don agajin gaggawa ta Ghana a bidiyon dake yaduwa wanda ya tabbatar da cewa ba’a Edo bane.
A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na amfani da wannan dama wajen yaɗa labarai, hotuna da bidiyon ƙarya kan abun.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Abumusa’ab J Aliyu ya wallafa wani rubuta da faifan bidiyo dake cewa
“Hukumomi Sun Fara Kama Matsiyatan da Suka Yiwa Yan Uwanmu Hausawa Matafiya Kisan Gilla A Jihar Edo…”

Shima wani shafin na facebook mai suna Nasiru Ibrahim Babajo ya wallafa irin wannan bidiyo inda ya rubuta cewa;
“Alhamdulillah An cigaba da kama yan lskan da suka yiwa Yan Arewa k!ssan gilla a Jihar Edo.”

Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba shafin rundunar ƴan sanda Najeriya inda ta tabbatar da kama mutum goma sha huɗu da ake zargi da hannu wajen kisan to amma babu hoto ko bidiyo.
Alkalanci ta duba wannan bidiyo da idon basira tare da gano tambarin ƴan sanda ƙasar Ghana a jikin rigunan ƴan sandan.
Haka zalika a jikin motar ƴan sandan an rubuta lambar 191 da 18555 waɗanda lambobin kiran ƴan sanda domin agajin gaggawa na ƙasar Ghana ne.

Lambar kira domin agajin gaggawa a Najeriya 112 ce.
Sakamakon bincike:
Bisa la’akari da kayan ƴan sanda da aka gani a bidiyon, tambarin dake ɗauke da Ghana, da kuma lambar neman agajin ƴan sandan ƙasar Ghana a jikin motar ƴan sandan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa bidiyon kame ne da ƴan sandan Nijeriya sukayi a Edo ƙarya ne.