BindiddigiBabu ‘Yan Arewa A Taron Hadin Gwiwar Najeriya Da...

Babu ‘Yan Arewa A Taron Hadin Gwiwar Najeriya Da Saudiyya?

-

Alakar Najeriya da kasar Saudiyya dadaddiyar alaka ce musamman kasancewar shekaru aru-aru musulman Najeriya na zuwa aikin hajji da umarah dama harkokin kasuwanci.

Batu:

Akwai wani faifai sauti mai tsawon minti daya da sakan talatin da biyar hade da hoto dake yaduwa a kafar sada zumunta ta WhatsApp dake ikirarin cewa akwai wani taro na musamman (summit) tsakanin Najeriya da kasar Saudiyya kuma babu Ko dan arewa daya a cikin wadanda zasu je taron.
Kadan daga cikin abinda ake cewa a sautin;  “ yallabai an tashi lafiya? Ni dai bana Najeriya for quite sometimes to amma nayi iyaka nawa, wannan summit din da za’ayi babu dan arewa Ko daya a ciki, kuma ya kamata ace mutanenmu gaskiya  blame game din da ake wa yan kudu ba laifun su bane laifun mu ne, hassada da kya shi ita ta dankaremu Yanzu ace za’ayi wannan a Saudiyya mu da muke da relationship  da Saudiyya tun kan Britain suzo mu arewa gashi abunda ake a business dinma anyi sidelining dinmu saboda da haka in da yadda za’ayi reaching out su manyan malamai da sukai karatu a Saudiyya Ko shi ambasada dake Saudiyya tunda shi dan arewa ne…
Haka zalika an sami wani faifan mai tsawon mintuna biyu da sakanni goma sha uku, da yake nuna cewa maganar da wancan yayi gaskiya ne.

Bincike:

Alkalanci mun tuntubi ofishin sakataren gwamnati dama ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya inda muka samo wata takarda da ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila inda yace binciken da aka gudanar ya nuna cewa wannan taro bai sami sahalewar hukumomin kasar Saudiyya ba hasalima shugaban wata hukuma mai suna NDCC ne ke kokarin damfarar jami’an gwamnati da kamfanin sa.
Takardar da fadar shugaban kasa ta rubuta zuwa ga sakataren gwamnatin tarayya yace ofishi na ya sami takardar gayyatar shugaban kasa zuwa kasar Saudiyya domin taro da kuma bada kyautar karramawa ga shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Takardar tace shugaban NDCC mai suna Miebaka Kenneth Adoki ne ya tura takardar gayyatar inda take cewa za’a gudanar da taron a tsakanin ranar 18 zuwa 24 ga wannan watan na Nuwamba a birnin Jidda dake Saudiyya.
A takaradar Gbajabiamila yace an gano cewa Mr. Adoki na kokarin zambatar fadar shugaban kasa ne kawai da sunan hukumar NDCC.

Sakamakon Bincike:

Sakamakon binciken Alkalanci ya tabbatar da cewa ikirarin da ake yadawa ba gaskiya bane domin kuwa taron da ake magana bai sami sahalewar gwamnatin Saudiyya ba, haka zalika gwamnatin Najeriya bazata shiga ko aike da kowa zuwa taron ba domin tana zargin ‘yan damfara ne suka shirya. Don haka wannan ikirari ya zama karya wato false a turance.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar