Fayyace abubuwaAlkalanci ta shaida wasu daga cikin munanan hare-haren Rasha...

Alkalanci ta shaida wasu daga cikin munanan hare-haren Rasha a Ukraine

-

 

Mutane da dama anan yankin namu wanda ya hada dani kai na na kallon ko sauraron yake-yake da akeyi tsakanin kasashen daga nesa. Mutane naji kuma na kallo amma baya ga mutuwar mutane, rusa gidaje ba kowa ne yake maida hankali kan sauran matsaltsalu da mutanen da ake haka suke ciki ba.

Shekara da shekaru muna jin batun kashe-kashe da kasar Isra’ila ke yiwa Falasdinawa, haka zalika wasu lokuta kungiyar Hamas na yin nata lokaci zuwa lokaci kan Isra’ila. Muna kallon yadda gidaje ke rushewa saboda hare-haren makami mai Linzami ko kuma jirgi maras matuki a Gaza da biranen Ukraine.
Zuwan da nayi Ukraine ya sanya na gane girman ta’asar rusa gina-gine da rasa rayuka da Falasdinawa ke fuskanta daga Isra’ila, ya kuma budemin idanu na yanayin zaman zulumi, mamaya da Isra’ila keyi domin kuwa iri daya ne da wanda Rasha keyi a biranen kasar Ukraine.
Kisan kare dangi da mamayar da Isra’ila keyi a Gaza shine irin abinda kasar Rasha keyi a Ukraine tun daga shekarar 2014.
Domin yadda Isra’ila ta saki bama-bamai a Gaza, West Bank shine ya faru a Butcha, Kyiv da sauran birane. Yadda Isra’ila ta mamaye yankunan Falasdinawa haka Rasha ta kwace Crimea.
A asubahin ranar 17 ga watan Yuni 2025 wanda ranar zamu shiga ƙasar Ukraine, Rasha ta kai wasu munanan hare-hare kan gidajen fararen hula a Solomianskyi kusa da Kyiv babban birnin ƙasar Ukraine.
Mun isa birnin Lviv da dare inda muka ganewa kanmu irin yadda mutane ke rayuwa kafin washe gari, akwai dai dokar hana fita da tsakaddare.

Ƙarfe 9am na safe kawai sai naji tsit mutane sun daina magana, an kashe radiyo, masu tafiya a waje sun tsaya cik har tsawon sakan sittin.
Na tambayi magajin garin Lviv Andriy Sadovyi ko me yasa haka? ya ce suna tsaida kome na minti ɗaya kullum domin tunawa da waɗanda suka mutu ta sanadiyyar hare-haren ƙasar Rasha.

Hoton Magajin garin Lviv Andriy Sadovy yayin jawabi ga ‘yan jaridu daga Afrika. (Hoto daga Ma’aikatar harkokin wajen Ukraine/ MYKHAILO PAKHOLIUK)

Na ziyarci makabartar da aka binne sojojin da suka mutu. An binne sojojin sama da dubu wadanda iya yan asalin birnin Lviv ne. Magajin garin Lviv ya ce kowanne birni na da makabartar da ake binne sojoji yan asalinsa da suka mutu a fagen yaki.

Hoton ziyarar makabartar da aka binne sojoji sama da 1000. Hoto MYKHAILO PAKHOLIUK

Na ziyarci inda ake sanyawa mutanen da suka rasa hannu ko ƙafa na roba da ake kira super human. Ana kokarin samar musu da hannaye ko kafa.

Hoton jawabi a cibiyar superhuman dake Lviv. (Hoto MYKHAILO PAKHOLIUK)

A cikin cibiyar superhumans ne muka fara jin amsakuwwar dake nuna yiwuwar kawo hari, inda muka garzaya zuwa daƙin ƙarƙashin ƙasa har saida aka bayyana cewa komai ya koma dai-dai.

Hoton ‘yan jaridu daga Afrika a dakin karkashin kasa domin yiwuwar kawo hari. (Hoto MYKHAILO PAKHOLIUK)

A daren ranar da muka isa birnin Kyiv da misalin kusan ƙarfe 2am na dare amsa kuwwa ta tashe ni wanda dole naje ɗakin ƙarƙashin ƙasa, na hadu da sauran yan jarida daga Afrika.

Editan Alkalanci Alhassan Bala, sauran yan jaridu a Afrika a dakin karkashin kasa misalin karfe 2am na dare a Birnin Kyiv na Ukraine. (Hoto Danjaridar Ivory Coast Stoney)

Washe gari mun kai ziyara guraren da Rasha ta taba mamaya kafin sojin Ukraine su tursasasu ja da baya.
Mun ziyarci wani coci a Butcha da aka binne mutane kusan sama da dari biyar, akwai kabari daya an binne mutane sama da dari.

Hoton inda aka binne mutanen da sojin Rasha suka kashe watan Fabrairu zuwa Maris 2022. (Hoto Ukraine MFA

Munje guraren da a da ginin gidaje ne mai hawa tara amma hare-hare ya rusa.
Mutanen Ukraine na ajiye tarihin duk abubuwan da suka wadanda ke faruwa.

Hoton ginin gidaje mai hawa tara da hare-haren Rasha suka rusa a 2022.

Mun ziyarci gadar da aka rusa don hana sojojin Rasha shiga birnin Kyiv, tuni dai an gina wata, yayin da aka bar wacce aka rusa a matsayin tarihi.

Hoton gadar da aka rusa data hana sojin Rasha zuwa Birnin Kyiv (Hoto Eduard Kryzhanivskyi, MFA Ukraine)

Mafi munin  gurin da muka ziyarta shine wanda ya faru ranar da muka isa, wato harin gidajen fararen hula a Solomianskyi, munga yadda harin jirage marasa matuka suka rusa gidaje 32 daga hawa na tara zuwa na kasa. Mutane 23 suka mutu yayin sa 27 suka jikkata.

Hoton daya daga cikin ginin da hari ya rusa na 17 ga Yuni, 2025. (Hoto Eduard Kryzhanivskyi, MFA Ukraine)
Ma’aikata na kokarin killace gurin tare da kwashe baruguzan ginin da ya fado.
Wasu hare-hare
Kwana daya bayan barina Kyiv, ina Warsaw kasar Poland naga labarin yadda Rasha ta kara kai harin jirage marasa matuka 352 da kuma makami mai linzami a birnin Kyiv da kuma Bila Tserkva. Sannan a ranar 29 ga watan Yuni, Rasha ta kara kai wani mummunan harin jirage marasa matuka sama da dari biyar ga biranen kasar Ukraine harda birnin Lviv wanda shine mafi nisa daga Rasha.
Yadda yakin ya shafi gurare.
Hukumomin kasar Ukraine da rahoton majalisar dinkin duniya ya tabbatar mutane nawa, makarantu, asibitoci nawa hare-haren Rasha ya shafa a Ukraine.
Akwai dai mutanen da suka rasa matsugunai sama da miliyan uku (3 million). Wanda yanzu sun zama yan gudun hijira.
Sama da makarantu dubu uku da dari shida (3,600) ne Rasha ta kaiwa hari.
Akalla asibitoci  dubu biyu da dari daya 2,100 Rasha ta kaiwa hari.
Tun daga watan Fabrairun shekarar 2022, hare-haren Rasha yayi sanadiyyar mutuwar fararen hula sama da dubu goma sha biyu (12,000) sama da dubu ashirin suka jikkata (27,000).
Majalisar dinkin duniya tace an sami karin rasa rayukan fararen hula a Ukraine da kashi talatin da bakwai (37%) daga watan Disambar 2024 zuwa Mayun 2025.
Me gwamnatin Ukraine ke bukata daga kasashen Afrika
Yayin ganawa da ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha ya ce Ukraine a shirye take ayi yarjejeniyar tsagaita wuta. Ya bayyana cewa wannan yakin ba batun shigar Ukraine kungiyar tarayyar Turai EU ko NATO bane fyace batu ne na shafe kabila da yaren mutanen Ukraine da Rasha ke yi ta hanyar wannan mamaya.
“Muna bukatar kasashen Afrika su taimaka wajen matsawa Rasha lamba don ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.”
Ministan Harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha da Editan Alkalanci Alhassan Bala. ( Hoto Eduard Kryzhanivskyi, MFA Ukraine)
Batun shiga Tarayyar Turai
Jakadiyar Tarayyar Turai a Ukraine Katarina Mathernova ta bayyana mana cewa, yanayin yadda Rasha ke shakulatun bangaro da tura kananan wakilai kan batun yarjejeniyar tsagaita wuta a Turkiyya ya nuna cewa ba da gaske take wajen kawo karshen yakin ba. Wanda ke nuna lokaci yayi da za’ayi amfani da diflomsiyya gaba daya.
Jakadiyar Tarayyar Turai a Ukraine Amb. Katarina Mathernová, yayin jawabi ga yan jaridu. (Hoto Ukraine MFA)
Ta baiwa shugabannin Afrika dake daukar Rasha a matsayin babbar kawa da suyi a hankali domin kuwa nan gaba kadan zasu iya yin dana sani, domin Rasha bata aikin banza dole sai mutum ya biya komai daren dadewa.
Ta yaya Ukraine ke kare kanta?
Duk da wadannan hare-hare da asarar dukiyoyi da rayuka da Ukraine ke samu daga Rasha, suma sojojin Ukraine na kaiwa Rasha hare-hare ta amfani da jirage marasa matuka. Wadannan hare-hare dai na yiwa Rasha itama barna duk lokacin da aka kaisu.
Alhassan Bala na cikin tawagar ‘yan jaridun Afrika da kasashen Czhechia, Poland, Ukraine da kungiyar tarayyar Turai suka hada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar