A ranar juma’a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da akafi sani da missile.
Duk da cewa akwai sarƙaƙiya kan inda aka kai harin na cewa guri ɗaya ne ko kuma gurare da yawa ne. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya ta tabbatar da harin Amurka a Jabo ta jihar Sokoto da kuma Offa ta jihar Kwara.
Shi dai wannan makami mai linzamin sunan shi BGM-109 Tomahawk.
Daga ina aka harbo shi?
An harbo shine daga cikin jirgin ruwa wanda a turance ana kiran shi shipborne sure face launch.
Kuma sunan inda aka harbo ɗin USS PAUL IGNATIUS (DDG 117).

A cikin Teku wato ruwan ƙasa da ƙasa nisan kilomita 200 daga gabar takun Najeriya.
Wato dai dakarun Amurkan sunyi amfani da jirgin ruwan yaki a ruwan ƙasa da ƙasa wajen ƙaddamar da harin.

Kudin hada makami ya kai dala dubu dari biyar ($500,000) yayind da farashin sa yana kai dala miliyan biyu ($2 million).
Tsayin ya kai taku goma sha takwas, wato aƙalla kusan mita shida kenan (5.56 m)
Makami mai linzamin BGM-109C/E WDU-36/Ba 690 nauyin sa ya kai kilogiram 310 yayin da nauyin kan makamin ke da nauyin kilogiram 120.
Gudun sa:
Yana iya gudun tsakanin kilomita 880 zuwa 920 a cikin awa ɗaya. Wato dai yana iya zuwa Sokoto daga Lagos cikin awa ɗaya da ‘yan dakiku.
