Zaɓe na nufin damar da jama’a ke da ita na zaɓar shugabannin su cikin lumana da gaskiya.
Amma a zahiri, a yawancin ƙasashen Afrika, wannan dama tana zama tushen rikici da tashin hankali, inda kowanne zaɓe kan zama lokacin tashin hankali, zargi da rarrabuwar kawunan ƴan ƙasa.
Meke janyo hakan?
Son mulki
Wannan matsala ta samo asali ne daga son mulki. Da dama daga shugabanni a Afrika na ƙanƙame kujerar mulki basa son sauka koda kuwa sun hau ta hanyar zaɓe wato damokraɗiyya ko kuma juyin mulkin wato mulkin soja.
Raunin tsarin damokraɗiyya
Raunin tsarin dimokuradiyya, kasancewar mulkin farar hula da ake kira damokraɗiyya ya kasance sabon abu a nahiyar Afrika idan aka kwatanta da wasu nahiyoyi. Shugabanni nayin kama karya tare da murɗe zaɓe.
Bari mu kalli yadda hakan ke faruwa a wasu kasashe.
Ƙasar Kamaru
Kamaru na daga cikin kasashen Afirka da ke da dogon tarihi na shugabanci marar sauyi. Shugaba Paul Biya, wanda ya hau mulki tun shekarar 1982, yana daga cikin shugabannin ƙasa da suka fi daɗewa a duniya.
A kowanne zabe, ana zargin gwamnatin da magudi, tsoratarwa, da kama ‘yan adawa.
Sakamakon haka, jama’a basa amincewa da sakamakon zaɓen, musamman a yankunan da ke neman ɓallewa – kamar yankin Anglophone.
Senegal
A Senegal kuwa, ƙasar ta kasance daya daga cikin ƙasashen Afrika dake da kwanciyar hankali amma a cikin shekarun baya-bayan nan rikice-rikice sun barke lokacin da tsohon shugaban kasa Macky Sall ya ɗage zaɓe.
Zanga-zanga ta yi ƙamari, yayin da aka dinga kama ‘yan adawa, tare da rasa rayuka.
Duk da cewa daga baya Macky Sall ya janye daga takara, abin da ya faru ya nuna irin rauni da rashin amincewa da tsarin siyasa da ke ƙara yaɗuwa a Afirka.
Uganda
A Uganda, shugaba Yoweri Museveni ya shafe fiye da shekaru 35 a kan mulki.
Duk da koke-koken ‘yan adawa kamar Bobi Wine, gwamnati tana ci gaba da murkushe zanga-zanga da kama masu adawa da ita.
Museveni ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar sau da dama, wanda ya soke iyakar shekarun ƙara tsayawa takara.
Jamhoriyar Damokraɗiyyar Congo
A Jamhoriyar Damokraɗiyyar Congo kuwa, zaɓe ya daɗe yana haifar da rikici saboda rashin tsari da rashin gaskiya.
Akwai zargin hannun wasu ƙasashe wajen taɓarɓarewar harkokin siyasa.
Zimbabwe
Yayin da a Zimbabwe kuma, bayan mutuwar Robert Mugabe, an yi fatan za a samu sabon salon amma tsohon tsarin tsawaita mulki da tasirin soja ya ci gaba da zama kamar tsohuwar hanya ta siyasa.
Burkina Faso, Mali, Chadi da Nijar
Su kuma waɗannan ƙasashe da sojoji sukayi juyin mulki a yanzu haka shugabannin sun sauya kundin tsarin mulkin ƙasashen domin ƙoƙarin su na daɗewa ko kuma ma dawwama a karagar mulki.
Dalilan Rikice-rikice Bayan Zaɓe a Afirka
Masana sun bayyana wasu muhimman dalilan dake janyo rikice rikice bayan Zabe a Afrika.
Wanda ya hada da Son mulki da tsawaita wa’adin shugabanci.
Rashin ‘yancin hukumar zaɓe da kotuna. Raunin tattalin arziki da talauci wanda ke sa matasa su zama masu saukin tada hankalin jama’a.
Rarrabuwar kawuna ƴan ƙasa saboda kabilanci da addini, wanda ke ƙara ruruta wutar rikici lokacin da sakamakon bai gamsar da wasu yankuna ba.
A yawancin kasashen Afirka, shugabanni sun shahara da son dadewa a kan mulki.
Wasu suna canza kundin tsarin mulki don cire iyakar wa’adin mulki, wasu kuma suna amfani da kotuna da jami’an tsaro don murƙushe ‘yan adawa.
Wannan hali ya sa mulki ya zama kamar gado ba amanar jama a ba.
Sakamakon haka, dimokuraɗiyyar tana durƙushewa, jama’a suna rasa amincewa da gwamnati, kuma tashin hankali bayan zaɓe yana karuwa.
