Fayyace abubuwaAbinda ya kamata ku sani dangane da alƙaluman ƙididdiga...

Abinda ya kamata ku sani dangane da alƙaluman ƙididdiga da NBS ke fitarwa

-

Lokaci zuwa lokaci dai hukumar ƙididdiga ta Najeriya wato NBS na fitar da alƙaluman tashin farashin kaya ko saukar su.

A lokuta da dama dai idan hukumar ta fitar da ƙididdiga mutane kan ƙalubalanci alƙaluman. Wasu lokutan mutane na ganin farashin wasu kaya sun sauka amma NBS na nuna cewa alƙaluma basu sauka, a wasu lokutan kuma suna ganin kamar ya kamata alkaluma su tashi sai kuma suga akasin haka.
Hukumar ta NBS na da abinda take kira da kwando wanda ke dauke da kayayyakin da take nema tare da samun farashin su duk wata.
A kwandon da ake amfani dashi wajen samun alƙaluma tsakanin 2009 zuwa 2024 akwai kayayyaki 720. To Amma hukumar ta sabunta kwandon daga watan Janairu 2024 inda yanzu kayayyakin sun kai 936.
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya wato NBS dai na zaɓar gidaje aƙalla dubu goma a sassan ƙasar inda ake basu littafin da zasu dinga rubuta farashin dukkan kayayyaki da suke siya kullum.

Yadde NBS ke samun alkaluma:

Habid Shehu Usman mataimakin shugaban hukumar ƙididdiga ta Najeriya. Inda ya bayyanawa Alkalanci cewa; Ana baiwa gideje sama da dubu goma a lungu da sako na Najeriya littafi domin su dinga rubuta komai da komai da suka siya a gidan har na tsawon watanni goma sha biyu.
Suna amfani da waɗannan litattafai ne wajen fitar da ƙididdigar kayayyaki musamman waɗanda suke da muhimmanci wajen fitar da ƙididdigar wata zuwa  wata.
Sannan hukumar na ziyartar dukkan kasuwanni a Najeriya duk wata domin samun farashin kayayyaki.
Haka zalika ya ƙara da cewa kaya na iya tashi a wani waje kuma ya sauka a wani waje.
“Hukumar na amfani da wanda yafi yawa wato Idan inda farashi ya hau ya fi inda ya sauka ko bai sauya ba. Wannan yasa wasu lokuta wasu na iya ganin kuɗin wasu kayayyaki basu sauka a inda suke ba amma suga sun sauka ko kuma sun sauka ace basu sauka ba. Hakan na faruwa idan ya kasance guraren da yawa an sami canji ko akasin haka. Haka zalika idan misali farashin masara ne kawai ya sauka ko dai ace cikin kwandon wasu sun ‘yan tsirari sun sauka babu tabbacin zaiyi tasiri wajen saukar alkaluma.”
Har zuwa shekarar 2024 hukumar ƙididdiga ta Najeriya na kwatanta farashin kayayyaki a shekara 2009 wajen fitar da alƙaluman ƙididdiga.
Wato misali suna kwatanta farashin robar ruwa a shekarar 2009 da farashin sa a lokacin da ake son fitar da alƙaluman ƙididdiga.
Wannan yasa tashin farashin ya kai har sama da kashi 34% a shekarar 2024.

Me yasa akace alƙaluma sun sauka a watan Janairu?

A farkon shekarar nan dai hukumar ta NBS ta fitar da sabbin alƙaluman ƙididdiga wanda ya nuna ya sauka zuwa kashi 24.48%.
Jami’in na NBS yace mutane na iya ganin cewa alƙaluman kididdiga sun sauka a watan Janairu wanda hakan ba yana nufin cewa farashin kayayyaki ya sauka bane bisa ƙididdiga.
“Tabbas farashin wasu kayan abinci sun sauka, to amma a alkaluman kididdiga bawai ya sauka bane. Abinda ya sa aka ga alkaluma sun sauka a watan Janairu shine, an sauya shekarar da ake amfani da ita na shekarar 2009  wanda yanzu aka koma amfani daga Janairun shekarar 2024. Sannan kayayyakin dake kwandon kididdiga waɗanda aka maimaita basu wuce 300 ba.
Mu daga ɓangaren mu saukar alƙaluman ba yana nuna cewa farashin kayayyakin sun sauka da kusan kashi goma ba. Hukumar ta NBS ta sauya shekarar da take amfani da ita wajen kwatanta alkaluman kididdigar farashin kaya wanda yanzu ya fara daga shekarar 2024.”
Mutane da dama dai sun zaci cewa alkaluman da aka fitar na watan Janairu na nufin saukar dukkan kayayyaki a Najeriya, to sai dan canza shekarar amfani da alkaluma ne suka sanya alkaluma suka sauka, ba wai farashin kayayyaki ne suka sauka gaba daya ba.
Labarai Masu Alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar ganawar Tinubu da Kwankwaso?

Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Tijjani Tj Hamza ya wallafa wani bidiyo inda yayi ikirarin cewa; “Kwankwaso ya gana da...

Shin an nemi wulakanta Shugaban Burkina Faso a Faransa?

A cikin ‘yan shekarun nan an cigaba da samun labaran karya musamman dake da alaka da kasar Burkina Faso. Ikirari: Wani...

Shin da gaske akwai ‘yar tsama tsakanin Tinubu da Kashim?

Tun bayan dawowar damakradiyya a shekarar 1999 za’a iya cewa samun rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa ba...

Waɗanne ƙasashe ake ganin suna goyon bayan kafa gwamnatin ƴan tawaye a Sudan?

Ayyana gwamnatin ƴan tawaye da jagoran RSF Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya yi a Sudan, ya zo a daidai lokacin...

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Karanta wannan

Ina gaskiyar ganawar Tinubu da Kwankwaso?

Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Tijjani Tj Hamza ya...

Shin an nemi wulakanta Shugaban Burkina Faso a Faransa?

A cikin ‘yan shekarun nan an cigaba da samun...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar