Tun bayan sa-in-sa da aka samu tsakanin Laftanar Yerima da Nyesom Wike a Abuja, ake ta yamaɗiɗin cewa wannan matashin soja ɗa ne ga Birgediya Janar Mohammed M Yerima mai ritaya.
Wani shafin Facebook mai suna Mikiya ya wallafa wannan labari wanda mutane sama da dubu daya da dari shida suka tofa albarkacin baki, yayin da sama da dubu daya da dari biyu suka kara wallafawa wato shares.

Sunansa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwa ne wanda aka haifa a Kaduna kuma ya girma a Kaduna da kuma Fatakwal na jihar Rivers, duk da cewa iyayensa ‘yan asalin garin Fune ne da ke jihar Yobe.
A shekarar 2011 ne Ahmed Yarima, mai shekaru 33 da haihuwa ya fara karatu a sashen koyar da aikin jarida a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Amma bai kammala karatu a ABU ba domin Yerima ya bar jami’ar Ahmadu Bello bayan shekara ɗaya bayan ya sami gurbi a NDA da ke Kaduna a 2012.
Yerima ya fito a matsayin Laftanar na sojan ruwa a shekarar 2017.
Menene hadin sojojin biyu?
Sahihan bayanai sun tabattar da cewa sojojin biyu sun fito ne daga jiha ɗaya, wato jihar Yobe, to amma akwai bambancin gari.
Birgediya Janar Mohammed M. Yerima mai ritaya wanda tsohon mai magana da yawun rudunar sojan kasar Najeriya ne, ya fito daga ƙaramar hukumar Bade, yayin da Laftanar A.M Yarima ya fito daga ƙaramar hukumar Fune.
Sai dai bayan dogon bincike da BBC da kuma jaridar PRNigeria suka gudanar, sun gano cewa wannan iƙirari ba gaskiya ba ne.
Binciken kuma ya tabbatar da mahaifin wannan matashin Laftanal A.M Yerima ba soja ba ne, harkokin kasuwanci yayi yayin rayuwarsa.
