BindiddigiIkirarin karya kan mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima

Ikirarin karya kan mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima

-

Hukunci: Ƙarya ne
Kasancewar babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta rawaito labarin, kuma babu faifon bidiyo ko sauti da ya nuna mataimakin shugaban kasa yayi wadancan kalamai. Haka zalika mai magana da yawun sa ya musanta hakan tare da cewa tun watan Janairu ake yada wancan labari a harshen Turancin Ingilishi ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin karya ne.

Ikirari:

Wani shafin Facebook mai suna DDL Hausa ya wallafa wani ikirari dake cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya koka kan yadda dan gidan shugaban kasa Seyi Tinubu ke masa shisshigi:
“Shishshiginka yayi yawa Kabarni Nayi Aikina Tunda Ba kaine kanaɗa Ni a matsayin Mataimakin shugaban ƙasa Ba, Shettima Ya Koka Kan Yunkurin Karbe iko daga Hannunsa Wanda Sheyi Tinubu yake ƙoƙarin yi a Halin yanzu. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira yunkurin kwace aikinsa, yana zargin dan Shugaba Bola Tinubu da yin ayyukan da ya kamata ya gudanar. Shettima ya ce Ban taɓa jin kaina a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba. Duk da cewa ya kamata in gudanar da muhimman ayyuka, dan Tinubu ne yake yin aikina.”
Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa.
Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa.
Wannan ikirari dai ya sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dari hudu tare da shares sama da dari uku.
Wani shafin na Facebook mai suna Gida-Gida TV shima ya wallafa irin wannan post a ranar 22/03/2025.
Shima shafin Gida-Gida TV ya sami comments sama da dari .
Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa.
Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi Stanley Nkwocha mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima  inda yace wannan magana ta masu yada karya ce kawai.

 Haka Zalika ya bayyanawa Alkalanci cewa tun watan Janairun 2025 irin wannan ikirari ke yaduwa a harshen turanci wanda tuni sun bayyana cewa labarin karya ne.

Sannan kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba sahihan gidajen jaridu don duba ko akwai wacce ta wallafa makamancin wannan labarai, to sai da Alkalanci bai samo komai ba.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima dai ya sha wakiltar shugaban kasa Bola Tinubu a ayyukan gwamnati a ciki da wajen Najeriya.
Hotuna da labarai a sahihan kafafen yada labarai ya nuna cewa yana gudanar da ayyukan na harkokin mulki yau da kullum.
A cikin Azumin 1446AH/2025 ne dai aka ga dan shugaban kasa Seyi Tinubu na ran gadi jihohi yana shan ruwa da matasa.

Sakamakon bincike:

Bisa ka sa samo labarin a wata sahihiyar gidan jarida na cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima yayi wadancan kalamai, da kuma bayanin mai magana da yawun sa, tare da samun labarai kala-kala dake nuna yadda mataimakin shugaban kasa ke ayyukan sa. Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta yanke hukunci cewa wancan ikirari karya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar