Tun bayan takaddamar masarauta a jihar Kano da ta sanya sarki Aminu Ado Bayero barin gidan Rumfa zuwa gidan sarki na Nasarawa akayi ta yada ikirarin cewar sarkin na zauna ne a makabarta.
Duk da cewa wannan ikirari an dade ana yinshi, a Yanzu kafar bin diddigi ta alkalanci zata binciki gaskiyar ikirarin.
A baya-bayan nan ma dai mataimakin gwamnan jihar Kano ya roki gwamnatin tarayya da ta dauke Sarki Aminu daga gidan na Nasarawa inda ya bayyana shi a matsayin makabarta.
Bincike:
Dafarko dai ita kalmar Nasarawa an Samar da ita ne daga Nasara(Turawa) kamar yadda Dr Nasiru Wada Khalil masani kan harkokin al’adun gidan sarki ya bayyana mana. Wanda hakan ke nuna cewa sai bayan zuwan turawa aka samar da wannan fadar.
Wannan fada dai an ginata ne a lokacin mulkin Sarki Muhammad Abbas wanda ya mulki jihar Kano daga shekarar 1894 zuwa shekarar 1903. Sarkin ya gina Wannan fada ne domin ganawa da Turawa(Nasara) akan harkokin shugabanci da kuma shakatawar sa a wancan lokacin. Sarkin ya rasu ne a wannan fada wanda hakan ya sa aka binne shi duk da cewa tarihi ya nuna an binne wasu Sarakuna a gidan sarki na Rumfa.
Hakan ya nuna cewa daga kan Sarki Muhammad Abbas ne aka fara binne sarakunan Kano a wannan fadar. Bayan Sarki Muhammad Abbas an binne sarakuna biyar a wannan fada wanda suka hada da, Sarki Shehu Usman da yayi mulki daga shekarar 1919 zuwa 1926. Daga shi sai Sarki Abdullahi Bayero da ya mulki jihar daga shekarar 1926 zuwa 1953. Sai Sarki Muhammadu sanusi na daya daga shekarar 1953 zuwa shekarar 1963.
A wannan shekarar ta 1963 ne sai Sarki Muhammad Inuwa yayi mulki kuma a ita ne Sarki Ado Bayero ya karbi mulki inda yayi shekaru 51 yana karagar mulki wanda dukkan su aka binne a wannan fada.
Idan akayi duba da wannan bayani an binne sarakunan Kano guda 6 a wannan fadar sarki dake Nasarawa.
Bincike ya nuna akwai dai sarakunan da suka taba zama na ‘yan kwanaki a gidan na Nasarawa to amma Sarki Aminu Ado Bayero shine wanda yafi dadewa zaune a gidan bayan da gwamnatin jihar karkashin shugabancin Abba Kabir Yusuf ta ce y’a tsige shi a matsayin sarkin Kano wanda batun ke kotu ya zuwa yanzu.
Sakamakon bincike:
Shin wannan yana nufin fadar ta Nasarawa ta zama makabarta?
Duk da cewa ba a gina fadar Nasarawa a matsayin makabarta ba amma binne wadannan sarakuna guda shida a wannan fada ya sa ta zamo makabarta wato inda ake binne sarakunan Kano Idan sun rasu wani abu kamar al’ada.
Bincike ya nuna babu wani Sarkin Kano da ya taba zama a fadar daya kai wata guda tun bayan fara binne sarakuna a gidan, wanda yasa kafar bindiddigi da tantance labarai ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari na cewa sarki Aminu na zaune a makabarta akwai kamshin gaskiya ne.
Labarai masu alaka:
- Shin dagaske ne hada tumatir, coffee da lemun tsami na sa fatar mutum tayi laushi?
- Ina Gaskiyar Harin Kunar Bakin Wake A CBN?
- Shin Sanata Barau Ne Ya Jagoranci Wucewar Kudirin Dokar Haraji Zuwa Karatu Na Biyu?