A cikin ‘yan makwannin nan dai an sami cacar baki tare da zarge-zarge tsakanin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti, wanda yanzu haka aka fara samun yaduwar labaran karya akan takaddamar.
Ikirari:
Akwai dai wani labarin dake yaduwa a kafar sada zumunta ta Facebook sosai inda wasu ke ikirarin shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya ba wa Sanata Natasha Akpoti hakuri kan abinda ya faru a tsakanin su cikin ‘yan kwanakin nan.
Misalin shafi mai suna ATP Hausa ya wallafa wani bidiyo a ranar 02/03/2025, tare da rubuta cewa “ Ina Mai Baiwa Sanata Natasha Hakuri A Kan Rashin Fahimtar Da Ya Faru Tsakanina Da Ita, Duk Abinda Na Yi Mata bataji dadi ba Ta Yi Hakuri – Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Akpabio”
Wannan wallafa ta sami mutane dabunnai da suka kalla.

Wani shafi ma mai suna Jaridar Arewa ya wallafa bidiyon ranar 02/03/2025 inda aka rubuta cewa; “Ina Mai Baiwa Sanata Natasha Hakuri A Kan Rashin Fahimtar Da Ya Faru Tsakanina Da Ita, Duk Abinda Na Yi Mata bataji dadi ba Ta Yi Hakuri – Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Akpabio.”
Wannan wallafa ta sami mutane sama da dubu hudu da suka kalla cikin kasa da awa biyu da wallafawa.

Wani shafin shima mai suna Daily Reports Hausa ya wallafa hoto dake dauke da Sanata Akpabio da Sanata Natasha inda ya rubuta cewa, “ Ina Mai Baiwa Sanata Natasha Hakuri A Kan Rashin Fahimtar Da Ya Faru Tsakanina Da Ita, Duk Abinda Na Yi Mata bataji dadi ba Ta Yi Hakuri – Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Akpabio.”

Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba bidiyo bada hakurin da akaji Sanata Akpabio na ba wa Sanata Natasha ya faru ne watanni bakwai da suka gabata wato a ranar 23/07/2024 yayin zaman majalisar.
Bidiyon dai wanda ke yaduwa shine wanda gidan Talabijin na Channels ya wallafa a shafin YouTube dinsa watanni bakwai da suka wuce wanda ya sami mutane da suka kalla sama da dubu dari da sittin.
A bidiyon da ke yaduwa dai anji Sanata Akpabio yana bayyana cewa yayi nadamar fadin kalamai na cewa a gidan gala ake daga murya, wanda wadannan maganganu basu yiwa mutane da dama da ita kanta Sanata Natasha dadi ba. Ya ce shima yana da uwargida kuma ya na da ‘ya’ya mata bazaiso wani yaci zarafin su ko kuma dakile kokarin su na zama wani abu ba.
kafar jaridar BBC pidgin ma ta wallafa labarin a ranar 23/07/2024.
Haka zalika babu wata gidan jarida sahihiya da ta rawaito wannan labari a matsayin sabon labari daya faru.
Sakamakon bincike:
Baya ga samo asalin lokacin da akai bidiyon da ake yadawa yanzu na bada hakuri da kuma kalaman shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio wanda yake bada hakuri kan batun kalamansa na gidan gala ga iya Sanata Natasha. Sannan ganin cewa bidiyon da kalaman tsofaffi ne kuma basu da alaka da sabuwar takadda tsakanin Sanatocin biyu yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.