Akwai wasu hanyoyi da zaku iya bi domin don kare kanku daga labarun karya da ake turawa ta dandalin tura sakwanni na WhatsApp.
1. Wa ya rubuta labarin?
Idan baku da tabbacin wa ya rubuta ko kuma daga Ina labarin ya fito to alama ce ta kuyi kaffa-kaffa.
Sannan kafin ku turawa wasu wato share: Ku tambayi wanda ya turo muku inda ya samo labarin, sannan ku duba bayanan labarin da kyau.
2. Ku tambayi kanku: shin zan iya tantance ikirarin?
Idan baku da tabbacin cewa ikirarin nada majiya mai kyau to kuyi a hankali wajen aminta dashi.
Kafin ku turawa wasu wato share: ku tambayi wanda ya turo muku, ko akwai wata kafar labarai sahihiya da ta ruwaito labarin, ku tabbata ba shafukan yada labarun karya ne suke yada labarin ba.
3. Labarin ya bata maka rai ko firgita ka?
Yawancin lokuta labaran karya na batawa mutane rai ko sanya mutane tsoron wani abu.
Kafin ka turawa wasu: ka tambayi kanka ko sakon na wasa da hankulan mutane musamman kan abinda suke tsoro ne? Da zarar kunga haka to ku duba bayanan da kyau.
4. Labarin na dauke da hotuna, bidiyo ko sauti mai ban mamaki ko razanarwa?
Yawancin labaran karya ana canza hotuna ko bidiyo koma faifan sauti domin cimma manufar sanya tsoro, fargaba ko tsanar wani abu.
Kafin ku turawa wasu: Ku duba da kyau ko an sauyawa hoton ko bidiyon daga yanayin sa na asali ko kuma an dakko ne daga wani abu daya faru a baya ko wani waje daban. Domin akan dakko hotuna ko bidiyon wani abu daya faru a wata kasa a nuna a wata kasar ya faru.
5. Ku tambayi kanku: Ina da tabbacin wannan labarin ba na yaudara bane?
Yawancin sakwannin karya ana iya tantance su ta hanyar amfani da shafukan sahihan gidajen jaridu ko shafukan kafafen tantance labarai, bindiddigi da bincike wato fact-checking irin kafar Alkalanci.
Kafin ku turawa wasu: Ku bincika don ganin ko an taba tantance labarin ko an taba bayyana shi a matsayin labarin karya.
Labarai masu alaka: