Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mulki kasar a matsayin soja tsakanin shakerar 1983 zuwa 1985. Sannan ya kara mulkar kasar a mulkin farar hula tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Ikirari:
Akwai wani ikirari daya yadu matuka wanda ke cewa tsohon shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari yace “Tsohon shugaban kasar ya ce yanzu haka ya sanya ‘yan haya a gidansa na Kaduna.
Buhari ya ce daga kudin hayar ne yake cin abinci da gudanar da harkokin rayuwarsa.”
Wannan ikirari ya sanya shakku a zuciyoyin mutane saboda kasancewarsa tsohon Janar na sojan kasa kuma tsohon shugaban kasa.
Domin kuwa fansho din wanda ya taba zama Janar a soja ya haura miliyan daya, banda batun kudaden da ake baiwa tsoffin shugaban kasa. Buhari dai kafin ya zama shugaban kasa ya tabbatar da cewa yana karbar kudade a matsayin tsohon Janar kuma tsohon shugaban kasa daga gwamnati. Duk da cewa a shekara 2016 fadar shugaban kasa tace ya daina karbar fansho daga sojojin kasa tunda ya zama shugaban kasa.
A shekarar 2022 wasu alkaluma daga hukumar RMAFAC ya nuna cewa ana baiwa tsoffin Shugaban kasa da mataimakan su kudade a matsayin na kula da kai.
Kafofin jaridu na Hausa dama na turanci sun dauki wannan labarin kuma ya yadu matuka.
Misali kafar yada labarai ta yanar gizo ta Legit.ng Hausa ta wallafa labarin a shafinta na Facebook kuma ya sami tofa albarkacin baki sama da dubu daya.
“Tsohon shugaban kasar ya ce yanzu haka ya sanya ‘yan haya a gidansa na Kaduna.
Buhari ya ce daga kudin hayar ne yake cin abinci da gudanar da harkokin rayuwarsa.”

Itama kafar yada labarai ta Aminiya ta wallafa wannan labari.
Haka zalika kafar yada labarai ta Liberty TVR ta wallafa
Kalaman Buhari: “Da Kuɗin Hayar Gidana Da Ke Kaduna Nake Sayen Abinci A Yanzu.”
Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin ya ci gaba da riƙe kansa.
Buhari, ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar a fadar Gwamnatin Katsina, inda ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba.
Bincike:
Binciken kafar bindiddigi da bincike tare da tantance labarai ta Alkalanci ya gano cewa kowacce gwamnati na ware makuden kudade wajen biyan tsoffin shugaban kasa da mataimakan su a kowacce shekara.
A dokar Najeriya dai ana baiwa kowanne tsohon shugaban kasa kudin da ya kai N350,000 yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa ke karbar N250,000 à matsayin kudin kula. Dokar ta amince kowanne ya sami kari da zarar shugaban kasa mai ci ya sami karin albashi.
Gwamnatin Bola Tinubu dai ta ware sama da Naira biliyan goma sha uku domin kula da tsoffin shugannin Najeriya da mataimakan su da sauran kusoshin gwamnati irin su tsoffin shugaban ma’aikata, manyan sakatarorin ma’aikatu da daraktoci da suka bar aiki.
Cikin wani bincike da jaridar PR Nigeria tayi ya nuna cewa maimakon gidaje uku da Muhammadu Buhari yayi ikirarin cewa sune ya mallaka takardar nuna abinda mutum ya mallaka da Buhari ya cike a shekarar 2015 ta nuna cewa Buhari ya mallaki gidaje biyar, gonaki, shanu 270, Tumaki 25 da sauransu.
Duk da cewa har yanzu ba’a sami takardar iya abinda ya mallaka bayan barin mulki ba.
Sakamakon bincike:
Binciken kafar tantance labarai ta Alkalanci ya gano cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da hakkin karbar fansho daga sojin kasa na Najeriya kasancewar ya taba zama Janar, haka zalika fansho da kudin kula saboda ya taba zama shugaban kasa.
Haka zalika yana da gonaki, dabbobi. Sannan yana da hannun jari a kamfanoni uku tare da filaye biyu. Hakan yasa za’a iya cewa kudin hayar da yayi magana na iya zama kudin dake taimakawa sauran kudaden shigar da yake samu, wajen gudanar da abubuwan rayuwa.
Wadannan alkaluma da bayanai dai sun sa kafar tantance labarai ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari na kawar da hankali ne wato misleading a turance.
Labarai masu alaka: