BindiddigiShin Nijar Zata Gina Katanga Tsakaninta Da Najeriya?

Shin Nijar Zata Gina Katanga Tsakaninta Da Najeriya?

-

Akwai dai zarge-zarge tsakanin gwamnatin Najeriya da Nijar tun bayan juyin mulki da sojoji sukayi a kasar, wanda ke rura wutar labaran karya dangane da kasashen biyu.

Batu:

Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani ikirari (archived here) a ranar lahadi 22/12/2024 inda ya rubuta cewa “ 🛑Nijar zata gina katanga mai tsawon Km 1497 a iyaka tsakaninta da Nigeria domin karfafa tsaro a kasar.”
W annan wallafa dai ta sami tofa albarkacin baki sama da dari uku kasa da mintuna talatin da wallafawa.

Bincike:

Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta tuntubi mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijar Amadou Ango Souley ((Responsable de la communication du Ministère des Affaires Étrangères auprès du Ministre)) data tambayeshi cewa baya ga zarge-zargen da sukewa gwamnatin Najeriya akwai shirin gina katanga tsakanin Nijar da Najeriya? Sai yayi dariya yace “wannan magana ce kawai babu wani shiri irin wannan, shirmen ‘yan kafafen sada zumunta ne kawai.”

Sakamakon Bincike:

Bisa bayanan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Nijar din na cewa babu wani shiri makamancin haka yasa kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar