A yan kwanakin baya dai wani tsohon abokin wasan shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo yana nuna sha’awar musulunci inda wasu har suka dinga yada cewa ya musulunta.
Batu:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani rubutu (archived here) daka ikirarin cewa “ Ronaldo ya gudanar da Umarar farko bayan ya musulumta“ baya ga wannan ikirari akwai wasu hotuna dake dauke da siffar Cristiano Ronaldo harma da wata mace tare dashi a gaban ka’abah sanya da ihrami wanda duk wanda zaiyi Haj ko Umrah sai ya sanya.
Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci tayi amfani da manhajojin duba hotuna inda ta gano cewa hoton dai kirkirarren hoto ne da akai amfani da fasahar AI wajen hadawa wanda dakyar mutane zasu iya banbance na karya da gaskiya wato “deep fake” a turance.
Haka zalika da kafar Alkalanci tayi amfani da sashen binciken hotuna na google babu wata sahihiyar kafar yada labarai a kowanne yare data wallafa hoton ma balle labarin.
Sakamakon bincike:
Bisa gano cewa hoton hadadden hoto ne da akayi amfani da kirkirarriyar fasahar AI aka hada abinda ake kira “deep fake” yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan labari dama hoton karya ne.