BindiddigiShin ‘Yan Kabilar Ijaw Na Jefa Jarirai Cikin Teku...

Shin ‘Yan Kabilar Ijaw Na Jefa Jarirai Cikin Teku Don Gwajin DNA?

-

Kabilar Ijaw sun kasance mutane ne dake zauna a yankin Neja-Delta musamman a jihohin Bayelsa, Ribas da Delta duk da cewa ana samun ‘yan tsiraru a jihohin Akwaibom, Edo da Ondo.

Tarihi ya nuna cewa duk mafi akasarin inda ‘yan wannan kabila ke zaune bakin teku ko babban kogi. Mutane ne da aka sansu da iya ruwa sosai domin kasancewar su mazauna bakin teku ko kogi.  Sana’ar wannan kabili ta kaka da kakanni itace kafun kifi wato su da kuma noma.

Batu:

Akwai wani mai suna Sulaiman Auwal Auwal Marshal daya wallafa wani faifan bidiyo (archived here) mai tsawon sakan 31 ya rubuta cewa “ YADDA KABILUN IJAW DAKE JIHAR BAYELSA SUKE GWAJIN DNA WATO GWAJIN KWAYAR HALLITA IDAN SUN HAIHU
A faifan bidiyon dai anga wata mata ta sanya jariri a cikin ruwa kuma ya kasance a sama ba tare daya nutse ba.

Bincike:

Binciken kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta fara da gano cewa an wallafa wannan bidiyo da irin wannan ikirari a harshen turanci a shafukan sada zumunta da dama.
Mun tuntubi wani dan kabilar Ijaw kuma ma’aikaci a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Kimiebi Ebienfa inda yace wannan ikirari na cewa ‘yan kabilar ta Ijaw na gwada kwayar halitta ta DNA ta wannan hanya a matsayin karya ne, ya kara da cewa tabbas a al’adar matan wannan kabila mace na sanya jaririnta a ruwan kogi ko teku domin fara koya masa ko gabatar dashi da ruwa domin jaririn ya koyi tare da iya ninkaya da wuri.
“Muna alfahari da kasancewar mu Ijaw kuma muna zauna a bakin ruwa wasu lokutan ma a saman ruwa. Zaka iya ganin ‘yan kabilar Ijaw sunyi gidaje a saman ruwa kuma suna zaune musamman inda ake kamun kifi da sauran su. Ina tabbatar da cewa a yanwancin lokuta da yaro yakai wata daya da haihuwa kai harma kasa da haka ana fara koya masa iyo ta hanyar sakashi a ruwa ba tare da rike shi ba.”
Akwai wani shafin Facebook mai suna Akpolokpolo D Creek MC shima ya wallafa wannan bidiyo inda yake cewa; “Mu ‘yan kabilar Ijaw ne cikin alfahari muna tabbatar da cewa haka muke yiwa jariran mu wanka. Mun tashi munga al’adar sanya jarirai cikin ruwan teku abar su zuwa yan mintuna.”
Wata matashiya da tayi ikirarin ‘yar kabilar Ijaw ce itama ta wallafa bidiyo a wani shafi mai suna Ijaw Blood inda take tabbatar da wannan al’ada ta sanya jarirai cikin ruwa domin su fara sabawa da ruwa.

Sakamakon Bincike:

Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci bata sami guri daya da aka tabbatar da cewa sanya jirarai cikin ruwa da ‘yan kabilar Ijaw keyi sunayi ne domin gwajin DNA face al’adar su ta fara koyawa yaransu ruwa tun suna jarirai da suka amince da. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar