BindiddigiShin maza basa samun kansar mama?

Shin maza basa samun kansar mama?

-

Ikirarin shaci fadi kan kansar mama Ko nono

1. Shin maza basa samun kansar mama?

Da dama dai mutane na ikirarin cewa kansar mama ta mata ce su kadai wato maza basa samunta domin galibi Idan anyi maganar mama ko nono tunani kan mata yake komawa.
To sai dai akasin hakan hukumar lafiya ta duniya WHO tace ana samun kaso akalla daya (1%) na maza dake samun kansar mama a fadin duniya, inda hukumar tace sauran kashi 99% duk matane ke fama da matsalar.
Da muka tuntubi kwararriyar likita kan abinda ya shafi kansa a asibitin kasa Dr. Hannatu Ayuba tace “Da dama mutane na ganin cewa kansar nono na mata ne kadai to amma ba haka bane wani kaso na maza har anan Najeriya suna fama da kansar nono shi yasa muke cewa koda kai namiji ne kuma kaji wani abu da baka yarda dashi ba a nononka Kaje gurin likita a duba”

Sakamakon Bincike:

Alkalanci ya yanke hukuncin cewa bisa wannan bincike wanda hukumar WHO ta tabbatar ta tabbatar da cewa maza ma na samun kansar mama don haka wancan ikirarin  shaci fadi wato myth ne kawai bashi da tushe.

2. Shin ‘yan mata basa samun kansar mama?

Bincike:

Mutane da dama na ikirarin cewa mata da suka manyanta ne kadai ke kamuwa Ko samun kansar mama wato su ‘yan mata dake ganiyar su basa samu.
Binciken hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Amurka wato CDC ya nuna cewa kashi tara (9%) na matan dake da kansar mama a kasar matane dake da shekaru kasa da 45.
Haka zalika kungiyar likitocin kansa ta Amurka ACS tace yiwuwar samun kansar mama bashi da alaka Ko nasaba da shekaru kawai dai lura tare da zuwa asibiti ana dubawa shine abu mai muhimmanci. Kungiyar ta jaddada bukatar mata su dinga zuwa gwaji koda kuwa a wanne shekaru ne domin kuwa kowacce mace na iya samun kansar da zarar ta balaga.

Sakamakon Bincike:

Bisa alkaluma dama bincike hukumomin lafiya na cewa kowacce mace da zarar ta balaga na iya samun kansar mama ya nuna cewa wannan ikirari shaci fadi ne wato myth.

3. Shin kullutu maras zafi a mama ba kansa bane?

Wasu matan na ikirarin cewa idan mace ta lallatsa mamanta kuma taji kullutu kuma baya mata zafi hakan na nuna ba kansar nono bace. To sai dai da muka tuntubi Dr. Hannatu Ayuba ta asibitin kasa a Abuja tace wannan ba gaskiya bane inda tace;
A farko-farko kullutin dake nono koda na sankarar mama ne ba dole bane ya kasance yana zafi ba Idan an tabashi, don haka duk wacce ta taba taji kullutu a mamanta to ta garzaya zuwa asibiti domin a duba a bincika a gani shin na kansa ne Ko kuwa bana kansa bane.
Haka zalika hukumar Kula da lafiya ta Amurka tace kashi 60% zuwa 80% na kullutu a nonuwa ba kansa bane to hakan ba yana nufin cewa kullutu maras zafi bana kansa bane domin an karkasa kullutan zuwa kashi da dama.

Sakamakon Bincike:

Sakamakon bincike da Alkalanci yayi ya nuna cewa wannan ikirari shaci fadi ne wato myth tunda binciken masana harkar lafiya ya nuna tare da bayyana cewa akwai kullutan kansa da basa zafi a farko-farko sai ta ta’azzara.

4. Gaskiya ne ba’a warkewa daga kansar nono?

Da dama daga mutane na ganin kansa a matsayin wani tarkon mutuwa wato da mutum ya kamu da ita sai dai ya jira lokacin mutuwa.
To sai dai kungiyar likitocin kansa ta Amurka tace kashi 90% na masu kansar mama da aka gano da wuri kuma aka fara magani suna rayuwa na tsawon akalla shekaru biyar a inda  Idan aka hada da wadanda ba’a gano da wuri ba suna iya samun kasa da haka.
Mun kara tuntubar Dr. Hannatu Ayuba ta asibitin kasa tace; Ba gaskiya bane ace ba’a warkewa daga wannan cuta ta kansar mama domin kuwa akwai bincike da magunguna da akeyi musamman Idan aka gano da wuri kafin ace kansar ta ta’azzara. 

Sakamakon Bincike:

Alkalanci ya gano cewa wannan ikirari bashi da tushe balle makama wato shaci fadi ne wato myth domin kuwa binciken masana ya nuna akasin wannan ikirari inda binciken ke nuna ana iya cigaba da rayuwa.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar