Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi tsarki ga musulman duniya, wanda ake sauyata a ranar Arfa wato 9 ga watan Zhulhijja kowacce shekara.
An dai sha rawaito cewa an baiwa shugabannin ƙasashen musulmai da manyan mutane kyautar wani ɓangare na rigar kamar yadda majalisar ɗinkin duniya ta tabbatar.
Cikin tonon silili na kundin Epstein dai an ga wasu saƙwannin email dake nuna cewa an taɓa baiwa mutumin da aka taɓa ɗaurewa da laifukan fyade ga ƙananan yara da baɗala iri-iri kyautar rigar Ka’aba.
Epstein ya karbi rigar ta Ka’aba a watan Maris din shekarar 2017 a cewar sakon email. Bayan ya kammala zaman gidan yari bisa laifin fyade.

Sakon email ɗin dai yayi zargin cewa Epstein ya karɓi kyautar bangarori uku na rigar ta Ka’aba.
Jikin rigar ta ciki, jikin rigar ta waje da kuma wani ɓangare da ba ayi amfani da shi ba.
Samun rigar Ka’aba dai na da matukar wahala da tsada. Sakwannin Email ɗin sun nuna cewa an kaiwa Epstein rigar Ka’aba har gida ne.
Babu dai wani rubutaccen dalili na kaiwa mai baɗalar kyautar rigar ta Ka’aba. Wato takardun tonon sililin basu bayyana dalilan bashi rigar ba.
An dai sanya ɓangarorin rigar a matsayin kayayyin fasahar zane wanda yasa hukumomin kwastom na Amurka suka bar su suka shiga ƙasar.

Takardun dai sun nuna wasu mutane biyu mace da namiji masu suna Abdallah Al maari da Aziza Alahmadi dake gabas ta tsakiya sune suka tura rigar daga Saudiyya zuwa Florida.
Wannan tonon silili dai na bankaɗo wasu sirrikan manyan mutane masu kuɗi da mulkin a ɓangarorin duniya.

