BindiddigiHoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun shafukan da suka fara wallafa hoton sun bayyana shi a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI, da kuma rashin samun daidaito na hoton kan shekarun Zohran Mamdami lokacin da ake iƙirarin an ɗauki hoto tare da bincike da manyan gidajen jaridu irinsi BBC, Washington Post da France24  daya bayyana hoton a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa Mamdami bashi da alaƙa da file ɗin Epstein da ake yaɗawa.
Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya.
Iƙirari:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Alhassan Mai Lafiya daya wallafa wani hoto dake iƙirarin cewa akwai magajin garin New York Zohran Mamdami a cikin file ɗin inda yayi rubutu kamar haka;
“An bankaɗo sirrin magajin garin New York (Zohran Mamdani) da mahaifiyarsa acikin file ɗin lalata na Epstein.”
Hoton ikirarin karya
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa hoton an fara yaɗa shi a wasu shafukan X da harshen Turanci wanda aka rubuta cewa hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
Wannan iƙirari ya samo asalin bayan billar sakon email na shekarar 2009 wanda a ciki akwai sunan Bill Clinton, Jeff Bezos da Mira Nair mahaifiyar Zohran Mamdami.
Alkalanci ta sanya hoton da ake yaɗawa a manhajar gano hotunan AI na Google inda sakamako ya nuna cewa an haɗa hoton ne ta amfani da ƙirƙirarriyar basirar AI.
Hoton sakamakon binciken daya gano hoton hadin AI ne
Haka zalika Alkalanci idan za ayi amfani da shekarun Zohran Mamdami ya zama cewa a shekarar 2009 shekarun sa 18 kenan wanda ya ci karo da abinda ake son nunawa a hoton.
Sannan duba da yadda aka ɗauki hoton akwai yanayi na da zaiyi wuya hakan ta faru.
Alkalanci ta gano cewa manyan gidajen jaridu irin su Washington Post, France24, BBC duk sun tantance hoton tare da bayyana shi a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI.
Sakamakon bincike:
Bisa samun shafukan da suka fara wallafa hoton sun bayyana shi a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI, da kuma rashin samun daidaito na hoton kan shekarun Zohran Mamdami lokacin da ake iƙirarin an ɗauki hoto tare da bincike da manyan gidajen jaridu irinsi BBC, Washington Post da France24  daya bayyana hoton a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa Mamdami bashi da alaƙa da file ɗin Epstein da ake yaɗawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna...

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai babban birnin ƙasar Nijar, shugaban...

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Karanta wannan

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano, ...

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar