Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la’akari yadda VOA ta taba wallafa hotunan a Disembar shekarar 2021 lokacin da mataimakin gwamnan ya je yiwa Kwankwaso ta'aziyya.Sannan tabbacin da aka samu daga jami’in gwamnati, Alkalanci ta tabbatar da cewa ikirarin cewa waɗannan hotuna na Nasiru Yusuf Gawuna da Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin sababbi ƙarya ne.
Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna a shafukan sada zumunta na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tare da Nasiru Yusuf Gawuna.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Dan Almajiri ya wallafa wannan Iƙirarin cewa Sanata Kwankwaso ya kira Nasiru Yusuf Gawuna gidansa inda suka gana.

Haka shima wani shafin mai suna Lamara Saraki shima ya wallafa wadannan hotuna da Iƙirari.

Masu yaɗa hotunan suna ta iƙirarin cewa “Kwankwaso ya kira Gawuna gidansa,” suna mai nuna cewa hotunan sababbi ne na wata ganawa da aka yi kwanan nan.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike don gano sahihancin hotunan da kuma lokacin da aka ɗauke su.
Da Alkalanci ta sanya hoton a Google lens sai sakamakon ya nuna cewa kafar yada labarai ta Muryar Amurka VOA ta wallafa hotunan tun ranar 23 ga watan Disembar 2021.

Wani shafin na Facebook ma mai suna Hon. Kamilu Aminu ya wallafa ranar ta 23 ga watan Disamba, 2021.
Wata hujjar da ke tabbatar da hakan ita ce yanayin hotunan, wanda ya yi daidai da zamanin ɓarkewar cutar Corona (COVID-19), inda ake iya ganin takunkumi fuska da aka yi amfani da su a wancan lokacin.
Don samun ƙarin haske, Alkalanci ta tuntuɓi Abdullahi Amir Kuma, wanda yana ɗaya daga cikin masu kula da harkokin midiya na gwamnatin Kano. Ya tabbatar wa Alkalanci cewa lallai waɗannan hotuna tsofaffi ne da aka yi a wancan lokaci.
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari yadda VOA ta taba wallafa hotunan a Disembar shekarar 2021 lokacin da mataimakin gwamnan ya je yiwa Kwankwaso ta’aziyya.Sannan tabbacin da aka samu daga jami’in gwamnati, Alkalanci ta tabbatar da cewa ikirarin cewa waɗannan hotuna na Nasiru Yusuf Gawuna da Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin sababbi ƙarya ne.
