BindiddigiKo Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen...

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Kasancewar ƙungiyoyin ta'addanci irin su JNIM, ISWAP, ISIL da Boko Haram na kai hare-hare a yankuna ƙasar Nijar tun tuni tare da kashe sojoji da fararen hula, sannan kuma babu wasu hujjoji da gwamnatin Nijar ta bayar dake nuna cewa ƙasashen Faransa, Benin da Ivory Coast na da hannu wajen harin Yamai yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa zargin bashi da tushe.
Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai babban birnin ƙasar Nijar, shugaban ƙasar Abdourahamane Tiani ya zargi ƙasashen Faransa, Jamhoriyar Benin da Ivory Coast da cewa sune suka kitsa harin.
Shin waɗannan ƙasashen ne suka kitsa harin?
Tun bayan juyin mulkin da Abdourahamane Tiani yayi a shekarar 2024 aka sami rashin jituwa tsakanin Nijar da ƙasashe makwabta da kuma Faransa.
Shugabannin mulkin sojin dai sun sha zargin ƙasashe da dama na cewa suna shirya tuggun hargitsa ƙasar ta Nijar ba tare da bada wasu hujjoji ba, wanda ƙasashen suka musanta.
Ɗaya daga cikin abinda Abdourahamane Tiani ya bada na yin juyin mulkin a Nijar shine kawo ƙarshen matsalolin tsaro dake addabar ƙasar ta Nijar shekara da shekaru.
Ƙungiyoyin ƴan taadda dai sun sha kai hare-hare ga sansanin soji da kuma garuruwan fararen hula.
Rahoton tsaron na Cibiyar nazarin tsaro ta duniya ya bayyana Nijar a  jerin ƙasashe wajen matsalar tsaro a duniya. 
A kwanakin baya ma dai ƙasar Benin da Nijar suka kori jakadun juna bayan rashin jituwa ta tsananta tsakanin ƙasashen biyu.
Tuni dai ƙungiyar ta’addanci ta ISIS ta ɗauki alhakin kai harin a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Nijar.
Nijar na fama da ƙungiyoyin ta’addanci irin su JNIM, ISWAP, ISIS da Boko Haram. Wani rahoto da aka fitar a watan Oktoban shekarar 2025 ya bayyana karuwar hare-hare kungiyoyin ta’addanci a Nijar.
Wani shafin Facebook mai suna Qibla Nijar dake goyon bayan shugabannon mulkin soji ya wallafa wani rubutu dake nuna matsalolin tsaro a Nijar ba wai a dinga zargin wasu kasashe ba.
Hare-hare a Nijar 
A watan Satumbar 2025 ma dai sai da ƙungiyar jihadi ta kashe mutane sama da 120 a Telliberi.
Haka zalika a watan Oktoba ƙungiyar ta’addanci tayi garkuwa da wani Ba Amurke. 
Ƙungiyar ta’addanci JNIM ta sha kai hare-hare a ƙasashen Burkina Faso (yankuna 11 cikin 13 na ƙasar), Benin, Ivory Coast, Mali (dukkan yankunan kasar) , Niger, Senegal da Togo.
Ko kwanakin baya ma sai da gwamnatin Nijar ta bakin Firaministan ƙasar cewa babu sojojin ƙasashen waje a ƙasar wanda binciken Alkalanci ya gano ba gaskiya bane. Bayan wannan harin da gwamnatin ta godewa sojojin Rasha ya tabbatar da
Sakamakon bincike:
Kasancewar ƙungiyoyin ta’addanci irin su JNIM, ISWAP, ISIL da Boko Haram na kai hare-hare a yankuna ƙasar Nijar tun tuni tare da kashe sojoji da fararen hula, sannan kuma babu wasu hujjoji da gwamnatin Nijar ta bayar dake nuna cewa ƙasashen Faransa, Benin da Ivory Coast na da hannu wajen harin Yamai yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa zargin bashi da tushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar