BindiddigiIna gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

-

Hukunci: Ƙarya ne
La'akari da cewa babu wannan labari ko hotuna a shafukan shugaban ƙasa, mai magana da yawun sa, da ma gidajen jaridu sahihai dake kawo rahoton da suka shafi wasanni, Sannan bisa la'akari da cewa babu inda aka rawaito shugaban Najeriya ya tarɓi tawagar ta Super Eagles bayan kammala gasar ta AFCON. Wannan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin da kuma hotunan dake cewa  shugaba Tinubu ya baiwa Super Eagles gidaje da motoci ƙarya ne.
Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Muhammad Bala Hamisu ya wallafa wasu hotuna da kuma iƙirarin dake cewa;  shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Yabawa Yan Wasan Nigeria Kyautar Gidaje da Motoci da Kudi.
Labarin karya dake yaduwa
Bincike:
Alkalanci tayi amfani da Google search inda ta gano yadda wasu shafukan sada zumunta suka wallafa hotunan tare da iƙirarin da harshen turanci. Sai dai duk shafukan da suka wallafa labarin babu guda ɗaya da yake sahihi.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafukan sada zumunta na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu inda ba a sami wannan labari ba. Sai binciken Alkalanci ya garzaya zuwa shafin Bayo Onanuga mai magana da yawun shugaban ƙasar Najeriya inda nan ma babu wannan labari.
Sannan Alkalanci ta ƙara da duba kafafen yaɗa labarai sahihai dake rawaito labaran wasanni amma babu wancan labari.
Gwamnatin Najeriya dai ta bakin ministan yaɗa labarai ta jinjina wa ƴan wasan na Super Eagles bayan da suka zo na uku a gasar, amma babu inda aka bayyana basu wata kyauta ta kuɗi, motoci ballantana gidaje.
Sakamakon bincike:
La’akari da cewa babu wannan labari ko hotuna a shafukan shugaban ƙasa, mai magana da yawun sa, da ma gidajen jaridu sahihai dake kawo rahoton da suka shafi wasanni, Sannan bisa la’akari da cewa babu inda aka rawaito shugaban Najeriya ya tarɓi tawagar ta Super Eagles bayan kammala gasar ta AFCON. Wannan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin da kuma hotunan dake cewa  shugaba Tinubu ya baiwa Super Eagles gidaje da motoci ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar