BindiddigiBidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun tabbacin cewa bidiyon da ake yaɗawa tsohon bidiyo ne kuma ɗan sanda da yayi holen wadanda ke bidiyon mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina ne ba Kano ba, sannab mai magana da yawun yan sandan Kano bai wallafa hoto ko bidiyon wadanda ake zargi ba duk da a wallafa tabbacin kama su, hakan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyon na yaudarar mutane ne.
Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai a jihar Kano.
Iƙirari:
Wani shafin Tiktok mai suna kafafocmero ya wallafa wani bidiyo da ƴan sanda ke holen wasu da sukai kisan kai inda suke faɗin yadda sukayi kisan. Inda aka sanya hoton mutane bakwai ƴan gida ɗaya da aka kashe a Kano tare da rubutun dake nuna cewa waɗanda sukai kisan ne.
Bidiyon ya sami mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da suka kalla.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa wannan bidiyo dake yawo akwai wani shafin Tiktok mai suna contentment9  daya wallafa shi a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2025 wato bara kenan.
Bidiyon ya sami mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar da suka kalla. Duk da cewa a hakan ma tsohon bidiyo ne ba a wannan lokaci akayi holen su ba.
Ɗan sanda dake holen masu laifin a bidiyon dai Alkalanci ta tabbatar da sunan sa Gambo Isa kuma yana aiki ne a rundunar ƴan sanda dake Katsina ba Kano ba.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa inda ya wallafa cewa rundunar ta kama mutum uku da ake zargin da kisan.
Wasu gidajen jaridu  da shafukan sada zumunta dai a Kano sun wallafa hotuna da sunayen mutanen da ake zargin da kisan mutanen bakwai ƴan gida ɗaya a jihar Kano.
Sakamakon bincike:
Bisa samun tabbacin cewa bidiyon da ake yaɗawa tsohon bidiyo ne kuma ɗan sanda da yayi holen wadanda ke bidiyon mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina ne ba Kano ba, sannab mai magana da yawun yan sandan Kano bai wallafa hoto ko bidiyon wadanda ake zargi ba duk da a wallafa tabbacin kama su, hakan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyon na yaudarar mutane ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Karanta wannan

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar