BindiddigiHotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa ganin cewa irin motar Almaz-Antey da ke ɗauke da makaman roka tana da nauyin fiye da tan 30. Amma a bidiyon, motocin suna tafiya ne a gefen hanya ba tare da ƙura ba ko wata alama sannan rashin daidaito na hotunan da kuma bidiyon da hotunan suka samo asali yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa Burkina Faso ta sami makamin rigar kariya daga harin sama daga Rasha da China karya ne.

 

Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo sun yaɗu sosai a kafafen sada zumunta a ranar 15 ga watan Janairun 2026.

Hotunan da bidiyon sun nuna cewa ana kai makaman rigar kariya ta harin jiragen sama masu zuwa Burkina Faso. Amma bincike ya tabbatar da cewa ba a sayar wa da Burkina Faso irin wannan kayan ba, kuma rundunar Africa Corps wani sashe na Ma’aikatar Tsaron Rasha da ke kula da ayyukan soja a nahiyar Afirka dake Burkina Faso da Mali ba sa amfani da su yanzu haka.

Hoton ya yaɗu sosai, musamman a dandalolin X, TikTok, da Facebook.

Hoton karya da ake cigaba da yadawa

Asalin hoton daga wani gajeren bidiyo mai daƙiƙoƙi goma aka samo shi, wanda ya nuna jerin motocin da ke ɗauke da makaman rigar kariya ta harin jirgin sama, da akayi ikirarin S-300 na Rasha ko HQ9 na ƙasar Sin, suna tafiya kan hanya a Burkina Faso. Wannan bidiyon ya samu kallo fiye da miliyan guda cikin awanni 24 kacal.

Masu sharhi sun ce hotunan na nuna cewa an ɗauke su a wuri guda. Don a ƙara ruɗa mutane, sai aka rage ingancin hotunan da gangan. 

A cewar masana, babu tantama cewa tura irin waɗannan makamai zuwa yankin Sahel zai nuna tasirin sojojin Rasha a yankin, kuma hakan na nufin Rasha na ƙoƙarin mamaye sararin samaniya a wasu wurare da ake kallon su da muhimmanci. Amma wannan hotuna da bidiyo na karya ne domin da fasahar AI aka yi

Bincike mai zurfi kan hotunan da bidiyon ya nuna rashin daidaituwa da dama. Misali, a cikin hoton jerin motocin, a wasu hotuna an nuna tayoyin gaba na ɗaya daga cikin motocin su biyu ne a gefe biyu, wato guda huɗu, a wasu kuma tayoyi shida, ko ma tayoyi biyu kacal, wanda ke nuni da amfani da AI wajen ƙirƙirar hoton.

Hotunan karya da ake cigaba da yadawa


Bincike ya tabbatar cewa irin wannan mota na da tayoyi huɗu ne a gaba, huɗu a baya; a duka ƙirar Rasha da ta ƙasar Sin. Wannan shi kansa yana nuna cewa akwai kurakurai da AI ya yi.

Bincike daga inda bidiyon ya samo asali a kafafen sada zumunta ya nuna cewa wasu shafukan sun bayyana cewa an yi amfani da AI ne wajen ƙirƙirar hoton. Wasu kuma ba su ambaci hakan ba. 

Hotunan karya da ake cigaba da yadawa


Yi Wa Hoton Kallon Tsanaki
A ƙarshe, idan aka kalli hoton da kyau, za a ga wasu abubuwan da ba su daidaita da juna ba. Na farko, inuwa da motar ta yi ba ta daidaita da siffar motar ba kanta. Masu wucewar da wasu daga cikinsu suna kan keke, ba sa kallon motocin, duk da kasancewar irin waɗannan manyan motocin a hanya abin jan hankali ne.
Sakamakon bincike
Bisa ganin cewa irin motar Almaz-Antey da ke ɗauke da makaman roka tana da nauyin fiye da tan 30. Amma a bidiyon, motocin suna tafiya ne a gefen hanya ba tare da ƙura ba ko wata alama sannan rashin daidaito na hotunan da kuma bidiyon da hotunan suka samo asali yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa Burkina Faso ta sami makamin rigar kariya daga harin sama daga Rasha da China karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar