Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda suke basu da tushe.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna “CLASSIC TV” ya wallafa wani labari mai taken: “DA ƊUMI ƊUMI: Aisha Buhari ta Amince da sheikh isah Ali Fantami Amatsayin wanda zata aura.”

wasu shafukan ma sun wallafa wannan labari kamar wannan shafin da wannan ma.
Wannan labari yana ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ta tofa albarkacin bakinsu, duk da cewa babu wani cikakken bayani ko hujja da shafin ya gabatar.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike don gano gaskiyar lamarin:
1. Rashin Sahihan Majiya: Binciken da aka gudanar a manyan gidajen jaridu da kafafen yaɗa labarai masu inganci (kamar BBC Hausa, Daily Trust, da sauransu) ya nuna babu ko ɗaya da ya wallafa wannan labari. Idan da gaske ne cewa mata tsohon Shugaban Ƙasar da fitaccen Malamin addinin suna shirin aure, zai zama babban labari da kowace kafa za ta ɗauka.
2. Yanayin Shafin: Shafukan da suka wallafa labarin sunyi shahara wajen wallafa labaran da ba su da tushe domin samun yawan masu kallo da ‘comments’. Irin waɗannan shafuka sukan yi amfani da kanun labarai masu jawo hankali ba tare da bincike ba.
3. Rashin Sanarwa: Babu wata sanarwa daga ofishin Aisha Buhari ko daga Sheikh Isa Ali Pantami ko iyalansu da ta tabbatar da wannan batu. A irin waɗannan al’amura na aure tsakanin manyan mutane, akan sami sanarwa ko ishara daga majiyoyi ta kusa, amma a nan babu.
4. Aisha Buhari a ranar da aka kaddamar da litattafin tarihin marigayi Muhammadu Buhari ta ce ba zata kara yin aure ba, guda daya da tayi ya isa.
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da cewa labarin ya samo asali ne kawai daga shafukan da ba su da sahihanci, kuma babu wata sahihiyar kafa da ta tabbatar da shi, Alkalanci ta tabbatar da cewa labarin ƙarya ne.
