Fayyace abubuwaMe yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

-

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso yamma dake fama da matsalolin yan bindiga dadi da barayin daji da masu satar mutane don neman kudin fansa.

Sai kuma  arewa ta tsakiya wadda a ‘yan shekarun nan ke fama da matsalolin barayin daji da masu satar mutane don neman kudin fansa da kuma kungiyoyi masu ikirarin jahadi. Hukumar U.S. Africa Command (AFRICOM) ta fitar da sanarwar cewa bisa ga umarnin shugaban kasar Amurka da sakataren yaki na Amurika  da hadin gwiwar hukumomin Najeriya sun kaddamar da hare-haren sama akan kungiyar yan ta’adda masu ikirarin jihadi ISIS a arewa maso yamma a jahar Sokoto a ranar 25th December 2025.

Labarin karyar kisan kare dangi ga Kiristoci ne da gwamnatin Amurka ke ta yayatawa ya haddasa wannan hari. Watannin da suka gabata shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi ikirarin cewa idan gwamnatin Najeriya bata dauki matakin dakatar da zargin kisan kare dangin da ake yiwa kiristoci a Najeriya ba zai kaddamar da hare-hare akan kasar domin magance kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu ikirarin jihadi a kasar.

Hukumomin Najeriya sun musanta labarin kisan kare dangi, haka zalika kungiyoyin kasa da kasa sun musanta wancan labarin na kisan kare dangi.

Su Waye ‘Yan IS Ko ISIS A Najeriya? 

Kungiyar ta’addanci ta ISIS ta samo asali daga kasar Iraq da Syria a karshe-karshen shekarar 2011. Burin wannan kungiya shine kafa daular musulunci, ta hanyar kaddamar da hare-hare, kisa, tsoratarwa da tayar da rikici da wasu sauran nau’uka na ta’addanci.

IS ko ISIS duk abu daya ne ana kuma kiran su da ISIL. Basu da wani bambanci a zahiri ko ta hanyar kaddamar da ayyukan su. Babu wani bayani ko hujja mai karfi da ta tabbatar da cewa ISIS/IS suna da rundononi kai tsaye daga kasar Iraq ko Syria a Najeriya.

Sai dai tun a shekarar 2015 kungiyar Boko Haram ta mika tayin mubaya’ar ta ga kungiyar ta IS inda kungiyar ta amince da tayin na kungiyar boko haram a lokacin kungiyar tana karkashin jagorancin Abubakar Shekau. Bayan amincewar da kungiyar tayi ta saka wa kungiyar sabon suna inda ta koma ISWAP (Islamic State West Africa Province). Daga baya a shekarar 2016 Boko Haram ta rabu gida biyu, IS ta amince da bangaren Abu Mus’ab Al-Barnawi wanda shi ya cigaba da jangorantar kungiyar ta ISWAP( Islamic State West Africa Province) bayan rabuwa da bangaren Shekau na kungiyar ta Boko Haram.

IS = Islamic State ISIS  na alaka da kungiyar ISWAP(Islamic State West Africa Province)  sansanonan su da ayyukan su suna arewa maso gabas a Najeriya musamman a dajin Sambisa da tafkin Chadi(Lake Chad) da Kamaru, Chadi da Nijar.

Kungiyoyin Ta’addanci a Arewa Maso Yammacin Najeriya

Arewa maso yamma na fama da hare-haren yan ta’adda, yan bindiga dadi da barayin daji dake satar mutane domin karbar kudin fansa. Sai kuma aka sami bayyanar sabuwar kungiyar yan ta’adda da ake kira LAKURAWA wacce ta bayyana a jahar Sokoto dake yankin na arewa maso yammacin Najeriya. Inda ita kadai ce ta bayyana a matsaying kungiya tilo da take da bakin haure daga kasashe kamar su Nijar, Mali da Burkina Faso a matsayin mambobi na kungiyar da kwamandodi inda suke da sansanoni a jahar ta Sokoto.

Binciken masa tsaro ya tabbatar da cewa Lakurawa sun zo yankin na Sokoto ne bayan da mutanen yankin Tangaza sun gayyace su domin kare su daga ‘yan fashin daji wato bandits. To amma daga baya suka rikida zuwa kungiyar ‘yan ta’adda wacce gwamnatin Najeriya ta ayyana.

Rahotannin baya-bayan nan sun tabbatar da cewa kungiyar ta LAKURAWA ta kara fadada hare-haren ta a wasu jahohin dake a arewa maso yamma musamman jahar Kebbi dake makwabtaka da jahar Sokoto inda wasu kananan hukumomin jahohin guda biyu suke makwabataka da juna kamar su TAMBUWAL, GUDU, BINJI da TANGAZA.

Karamar hukumar Tambuwal na daya daga cikin kananan hukumomin dake makwabtaka da jahar kebbi sai dai wannan karamar hukuma bata daga cikin kananan hukumomin dake fama da matsanancin rashin tsaro a jahar ta Sokoto.

Garin Jabo na karkashin karamar hukumar Tambuwal inda yana daya daga cikin wuraren da kasar Amurka ta kai hari a daren alhamis data gabata, Sai dai makaman da aka harba a garin na Jabo sun sauka a bayan garin na Jabo inda ya kasance gonaki ne na mutanen garin haka kuma ba a samu wani rahoto rasa rai ba daga yankin na Jabo.

Akwai rahoton da ke yaduwa na cewa karamar hukumar Tangaza ta kasance daya daga cikin wuraren da kasar Amurka ta kai harin na daren Alhamis da ta gabata. Tangaza na daya daga cikin kananan hukumomin da LAKURAWA suke da karfi sosai da kuma sansanonin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Bayan kaddamar da harin hukumomi a karamar hukumar ta Tangaza sun bayyana cewa tabbas ankai hari a wasu daga cikin sansanonin ‘yan ta’addan LAKURAWA.

Masana tsaro sun tabbatar da cewa akwai hadin gwiwa ko alaka tsakanin kungiyoyin ‘yan ta’adda a arewa maso yamma da kungiyar ISIS.

Kungiyoyin Ta’addanci A Arewa Ta Tsakiya

Yankin shima yana fama da matsalolin barayin daji (Bandits) da kungiyoyi masu ikirarin jihadi irin su MAHMUDAWA, ANSARU(Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan) sai dai wayan nan kungiyoyi ta bayyana cewa basu da alaka da kungiyar IS/ISIS sai dai rahotanni sun nuna cewa suna biyayya ga kungiyar JNIM(Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin) wadda ita ke wakiltar AL-QAEDA a yankin Sahel da yammacin Africa.

ANSARU(Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan) ta fice daga cikin kungiyar boko haram a shekarar 2012 inda suka bayyana dalilin ficewar su daga kungiyar akan cewa ta sauka daga manufofin da aka kafata tun farko, ANSARU ta fice daga kungiyar Boko Haram tun kafin suyi mubayi’a ga IS/ISIS a shekarar 2015.

ISWAP(Islamic State West Africa Province) ita ma ta raba gari da kungiyar ta Boko Haram bisa ga dalilin da ANSARU ta dogara dashi akan ficewar ta daga cikin kungiyar ta Boko Haram.

Harin da aka kai a daren Alhamis a jahar kwara da take arewa ta tsakiya a Najeriya ya fada a tsakiyar garin Offa wacce karamar hukuma ce a jahar Kwara wanda sanadiyar haka harin yayi illa ga wasu otal otal guda biyu da kuma wani bangare na masallacin idi dake garin na Offa. Bayan haka ansamu burbushin ababen fashewa a wata gona a yankin da ake kira Oro kilomita 25 kilometers daga garin na offa. 

Me yasa Sokoto?

Na farko, shakarun baya ne dai aka sami matasa suka kashe wata kirista mai suna Debora da ake zargi da batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) a Sokoto wanda labarin ya yadu matuka a kafafen yada labarai na Najeriya da kasashen waje. 

An sha samun masu sharhi na kawo misali kan kisan Debora a matsayin misalin yadda rayuwar kiristovi ke cikin hadari.

Na biyu kasancewar kungiyar LAKURAWA na da alaka da ISIS wanda a harkokin kasa-da-kasa na nufin cewa suma ISIS ne wanda kuma suke a jihar Sokoto yasa Amurka kai hari Sokoto. 

Duk da cewa masu sharhin kan tsaro da dama na ganin ba Sokoto bane ya kamata a fara da.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Wasu shafukan da suka dinga yaɗa ƙage da labaran ƙarya a shekarar 2025

Shekarar 2025 dai ta kasance shekarar da aka sami wasu shafukan sada zumunta da kaso mafi yawa na abubuwan...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar