Fayyace abubuwaGaskiyar abin da ke tattare da yarjejeniyar hukumar FIRS...

Gaskiyar abin da ke tattare da yarjejeniyar hukumar FIRS ta Najeriya da Faransa

-

Biyo bayan sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar haraji tsakanin Najeriya da Faransa a wannan watan na Disamba, an yi ta cece-kuce da nuna damuwa a kafafen sada zumunta. Babban abin da mutane ke tsoro shi ne: shin Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) za ta miƙa mabuɗin bayanan masu biyan haraji na Najeriya ne ga gwamnatin ƙasar Faransa ko yaya?

Saboda yaɗa jita-jitar da ake ta yi, yana da kyau a fahimci mene ne ainihin abin da aka sanya wa hannu, da kuma inda ruɗanin ya samo asali.

Yarjejeniya

Yarjejeniyar ta fahimtar juna, wato (MoU) da aka sanya wa hannu tsakanin hukumar tattara haraji ta Najeriya FIRS da hukumar tattara haraji ta ƙasar Faransa (DGFiP) an bayyana ta a hukumance a matsayin ba da horo kan yadda za a yi amfani da fasahar zamani.

A sauƙaƙe, wannan yarjejeniya ce ta musayar ilimi. Faransa za ta bayar da horo ne ga ma’aikatan hukumar FIRS kan yadda ake gudanar da hada-hadar kuɗi da tattara haraji ta hanyar fasahar zamani da kuma zamanantar da tsarin karɓar haraji.

Hukumar FIRS ta fito fili ta bayyana cewa wannan yarjejeniya ba ta bai wa Faransa damar shiga rumbun bayananta ba, ko kayan aikinta na na’ura ba, ko bayanan sirri na masu biyan haraji. Idan mutum yana karɓar albashinsa a Legas kuma yana kashewa a Abuja, bayanansa suna nan daram a cikin gida ba wai za a tura su zuwa ƙasar Faransa ba ne ko kuma a ba Faransar damar ganin bayanan.

Inda Ruɗanin Yake: Tsarin Ba Da Bayanan Haraji na Duniya
Mafi yawan tsoron da ake ji ya samo asali ne da haɗa wannan sabuwar yarjejeniyar horo da wani tsohon tsari da ƙasashen duniya suke kai da ake kira ‘Automatic Exchange of Information (AEOI)’. Tsari ne da ƙasashen duniya suka samar ta yadda suke musayar bayanan haraji daga mutanen da suke zille wa biyan haraji a ƙasashensu wato tax evasion.

Njaeriya dai ta ƙulla yarjejeniya da wasu kasashen duni wanda Faransa ta kasance ta baya-bayan nan, wadda yarjejeniya ce da ta ƙunshi ƙasashe sama da 100 da suke musayar taƙaitattun bayanan banki, kamar adadin kuɗin da ke cikin asusun banki da kuma suna da ƙasar mai asusun don yaƙi da ƙin biyan haraji. Amma tsarin ba ya nufin bibiyar bayanan sirri na mutane.

A ƙarƙashin wannan tsohuwar yarjejeniya, idan ɗan Najeriya yana da ɓoyayyen asusun banki a Paris, hukumomin Faransa za su sanar da hukumar FIRS, ko ita ma Najeriya ta sanar da Faransa idan ta ga wani ɗan ƙasarta da irin wannan asusun a Najeriya.

Sai dai wannan yana shafar waɗanda ke ɓoye dukiya a ƙasashen waje ne kawai, ba wai gama-garin mutane da ke ƙasar Najeriya da Faransa ba. Hakan ba ya nufin Faransa tana duba bayanan wanda ke da shagon sana’a a Kano ko ma’aikacin gwamnati da ke Enugu.

Abin da Mutane Suke Tada Jijiyoyin Wuya A Kai

Jita-jitar cewa za a dinga kwasar bayanan ‘yan ƙasa, ƙarya ce. Abin da masu sharhi suke jayayya a kai shi ne, dogaro da ƙasashen waje game da sha’anin horarwa kan muhimman manhajojin na’ura na iya haifar da matsala ko buɗe hanyar da za a samu damar shiga rumbun bayanan tattalin arziƙin ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

Sharhi: Sabuwar yarjejeniyar ta shafi bayar da horo kan yadda za a yi amfani da fasahar zamani, ba leken asiri ba. Matuƙar mutum ba shi da wasu miliyoyin kuɗi da ya ɓoye a asusun bankin Faransa, bayanan harajinsa suna nan a tsare tsakaninsa da gwamnatin Najeriya kawai, ba ruwan ƙasar Faransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ƙarya ne: Nasiru El-Hikaya baya cikin waɗanda VOA suka kora a shekarar 2018

Akwai wani shafin Facebook mai suna Gimbiyar Hausa ya wallafa wani iƙirari kan cewa ta kori wani ɗan jaridar...

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Karanta wannan

Ƙarya ne: Nasiru El-Hikaya baya cikin waɗanda VOA suka kora a shekarar 2018

Akwai wani shafin Facebook mai suna Gimbiyar Hausa ya...

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar