Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado da bangaren Sarki Muhammadu Sanusi.
Iƙirari:
Wani labari yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta Facebook, musamman daga wani shafi mai suna MALAM KHAN NEWS, wanda wasu shafukan suka yada, inda aka yi iƙirarin cewa Janar Christopher Musa, Ministan tsaron Najeriya, ya fitar da umarni mai cewa:
“Aminu Ado Bayero Yazo ya samini nan da awa 24 kuma shi kadai, Saboda shi ba SARKI ba ne a wojen mu.”
Wannan wallafa ta jawo cece-kuce tare da samun martani daga mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin kamar gaskiya ne.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike kan wannan iƙirari domin gano gaskiyar lamarin.
Da farko, Alkalanci ta tuntuɓi Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, Sakataren yaɗa labaran Sarki Aminu Ado Bayero, domin jin ta bakinsa. Ya tabbatar da cewa labarin ba gaskiya ba ne, inda ya ce:
“Mu ma haka muka tsinci labarin nan ana yaɗa shi, amma ba gaskiya ba ne. Magana tana gaban kotu, don haka ba a yanke hukunci ba har yanzu. Saboda haka wannan labarin ba gaskiya ba ne.”
Na biyu, Alkalanci ta gudanar da bincike a manyan kafafen watsa labarai na gida waɗanda aka sani da kawo sahihan labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, amma babu ko ɗaya da ya rawaito wannan labari. A al’adance, umarni mai ƙarfi irin wannan daga babban jami’in tsaro kamar Christopher Musa zai kasance babban labari a jaridun ƙasa.
Na uku, salon yadda aka rubuta labarin a Facebook yana ɗauke da kurakurai da kuma kalaman da ba su dace da tsarin magana na manyan jami’an gwamnati ba.
Sakamakon Bincike:
Bisa rashin gamsasshiyar shaida ta labarin da ake yaɗawa, da rashin samunsa a sahihan gidajen jaridu, tare da bayanin ƙaryatawa daga bakin Sakataren yaɗa labaran Sarki Aminu Ado Bayero, Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, Alkalanci ta tabbatar da cewa labarin ƙirƙirarre ne kuma ba shi da asali.
