Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu kasashe domin cimma wata manufa.
Ɗaukar yaɗa labaran ƙarya wata manufa ce da dabarun manyan ƙasashe wajen farfaganda tare da neman faɗa aji.
Editn kafar tantance labarai ta Alkalanci Alhassan Bala ya tattauna da Fauziyya Kabir Tukur wacce kwararriyar ƴar jarida ce kuma mai bincike kan labaran ƙarya daga ƙasashen waje da ake kira FIMI a turance.
Me yasa ake samun yaɗuwar labaran ƙarya a ƙasashen Sahel da Afrika ta yamma musamman a harshen Hausa?
Ana samun yaɗuwar labaran ƙarya ne saboda yadda ake lura mutane na don jin labari, kuma ana amfani da yanayin da suke wajen ƙirƙirar labaran ƙarya da yaɗa shi. Misali a Najeriya akwai matsalar bambancin ƙabila da addini, dan haka abu ne mai sauki ayi amfani da wannan kafa wajen yaɗa labaran ƙarya domin cimma manufar raba kan mutane ko haddasa yaƙi.
A kwanakin baya-bayan nan shugaban Amurka ya fito ƙarara yace ana kisan ƙare dangi wa Kiristoci wanda mutane da dama suka yaɗa ba a Najeriya kaɗai ba a sauran ƙasashen duniya. Wannan labari duk da bincike ya tabbatar da cewa ƙarya ne amma mutane da dama sun yarda dashi kuma sun yaɗa shi.
Wannan shine babban misali na kusa dangane da labaran ƙarya daga wata ƙasa da ake yaɗawa dangane da wata ƙasa a yammacin Afirka.
Ta waɗanne hanyoyi ake bi wajen yaɗa labaran ƙarya musamman wanda yake daga wata ƙasa FIMI?
Ƙasashen Afrika basa yaɗa labaran ƙarya zuwa ƙasashen yamma. To amma zaka ga wasu manyan ƙasashen yamma na amfani da shahararrun mutane ko ƴan jaridu wajen yaɗa farfagandar su ko labaran ƙarya. Bincike ya nuna cewa akan ɗauki nauyi su shahararrun mutane wato influencers wanda sune zasu san yadda zasu rubuta ko isar da labaran ƙaryar ta yadda mutane zasu yi saurin karɓa. Sukanyi amfani da labarai masu sosa zuciya wato emotions wajen isar labaran ƙarya da suke so, wanda cikin ɗan ƙanƙanin lokaci zaka ga mutane sun amince da shi wanda koda an tantance an bayyana gaskiyar labarin sai kaga baiyi tasirin yadda labaran ƙarya yayi ba.
Waɗanne Ƙasashe ne suke yaɗa labaran ƙarya a yankin yammacin Afirka da Sahel?
A gaskiya yanzu dai Rasha da Amurka sune suke kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya. Duk da cewa ana zargin China da cewa ita ma tana yi amma nata ya sha banban.
Misali munga yadda Rasha tayi amfani da labaran ƙarya ta shiga Mali, wanda yakai Mali ta ɗakko sojojin hayar Wagner Group. Sannan Mali ta kori sojojin Faransa ko ace Faransa gaba ɗaya. Mun ga yadda Rasha tayi amfani da ƴan jaridu da ƴan ƙungiyoyin fararen hula na Mali wajen tallata manufofin ta. Sannan Rasha ta siye ƴan rajin haɗin kan Afrika wajen tallata manufofin Rasha a ƙasashen Afrika.
Ko lokacin da akai juyin mulkin ƙasar Nijar ai munga yadda suka dinga ɗaga tutar Rasha.
Wato Afrika kamar tsaleliyar budurwa ce ga manyan ƙasashen nan kowanne yana son yayi wuce da ita.

Me yasa Rasha tafi son ayi juyin mulki wato mulkin soja a Afrika sama da mulkin farar hula?
Rasha na ganin cewa zata fi samun goyon baya da kuma juya shugabannin ƙasashe ƙarƙashin mulkin soja sama dana farar hula domin mulkin soja duk abinda shugaban ƙasa yayi dai-dai ne, ba kamar mulkin farar hula ba.
Rasha na son ta sami gindin zama da faɗa aji a ƙasashen Afrika.
Tsakanin Rasha da Amurka wanne yafi ɗan dama-dama wajen yaɗa labaran ƙarya?
Wannan tambayar na da sarƙaƙiya sosai domin kowanne daga cikin su yana son cimma wata manufar ne. Yana son tabbatar da faɗa aji da nuna iko. Kuma kowanne daga cikin su tsarin sa daban.
Rasha na nuna wa Afrika cewa ita saliha ce, tazo ne ta cece ƙasashen. Ita kuma Amurka tana nuna duk abinda tace ko take so shi za ayi. Dukkan su dai abu ɗaya suke nema wato arzikin ƙasa da zasu kwasa su wuce dasu.

Dole a ƙara tashi tsaye wajen yaƙi da labaran ƙarya, musamman a ƙasashenmu na Afrika. Wannan hira ta ƙayatar.
Muna godiya matuƙa.