Yayin da matasa a Afrika musamman a Najriya ke cigaba da kokarin samun tallafin karatu, aikin yi, horo ko neman kudi a kasashen waje, to sai dai akwai manyan kalubale a yanzu musamman dangane da wasu kasashe.
Libya
A Afrika dai binciken majalisar dinkin duniya da tarayyar turai EU ya nuna kasar Libya a matsayin kasa mafi hatsari ga bakin haure ko ‘yan cirani.
Libya ta zama matattarar masu safarar mutane, bauta, da kuma yiwuwar rasa rai.
Wasu ‘yan Afrika na amfani da Libya wajen kokarin tsallakawa Turai ta barauniyar hanya.
Najeriya dai na cigaba da kwaso ‘yan kasar da suka makale da Libya. Duk da wannan kokari na hukumomin Najeriya na nunawa ‘yan kasar hatsarin dake tattare da zuwa a Libya wasu ‘yan kasar na tafiya.
Rasha
A shekarar 2024 wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AP ya fitar wanda gidan jaridar The Mascow Times ya wallafa a shafin sa ya nuna yadda mahukuntan Rasha suke amfani da ‘yan Afrika.
Rahoton ya bayya cewa ‘yan Afrikan galibi mata anyi amfani da yaudarar za a basu tallafin karatu ko kuma albashi mai tsoka, wanda bayan sun isa sai a karbe fasfo din su da kuma kais u masana’antar kera jirage marasa matuka.
A wannan shekarar ta 2025 ma gidan jaridar BBC ya wallafa bincike kan amfani da ‘yan Afrika wajen kera jirage marasa matuka da Rasha ke amfani dasu wajen yakar Ukraine.
A kasar Sudan ta Kudu ma’aikatar ilimin kasar ta sanar da batun tallafin karatu a Rasha wanda kuma daliban da suka tafi aka kaisu wajen kara jirage marasa matuka a Rasha.
Akwai dai ‘yan Afrika da dama da suka rasa rayukan su yayin da suke yaki. Yayin da wadanda sukai sa’a suke a gidajen yarin fursunonin yaki a kasar Ukraine bayan an kamasu.
Akwai dai dan Najeriya, Ghana, Somalia da ‘yan Kenya da ke gidajen yarin wanda hukumomin kasar Rasha basu taba sanya su a cikin musayar fursunonin yaki ba.
Me Gwamnatocin ƙasashen Afrika ke cewa?
Kenya
Hukumomin kasar Kenya sun tabbatar da samun ƴan ƙasar mutum 200 da ke taimakawa Rasha a yaƙinta da Ukraine inda ministan harkokin wajen ƙasar Musalia Mudabadi ke cewa cikinsu har da tsaffin sojin ƙasar da suka yi ritaya.
Wannan labara dai za a iya cewa ya kara tabbatar da bayanan da ke cewa Rasha na amfani da tarin ƴan ƙasashen Afrika a matsayin Sojin haya don yi mata yaƙi a Ukraine.
Ministan harkokin wajen na Kenya ya ce kaso mai yawa na Sojojin ƙasar da sauran fararen hular da ke aikin sojin hayar a Rasha, tilasta su akayi yin yaƙin, kuma wasunsu an saka su a sashen da basu da ƙwarewa a kai.
A kwanakin baya ne dai shugaban Kenya William Ruto ya aikawa kasar Ukraine buƙatar sakin ƴan ƙasar da aka kama a fagen daga yayin wannan yaƙi a ɓangaren Rasha.
Afrika Ta Kudu
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Ramaphosa ya bayyana cewa akwai ‘yan kasar 17 yanzu haka da Rasha take amfani dasu wajen yakin Ukraine.
Yace an yaudari ‘yan kasar ne ta amfani da alkawuran biyan albashi mai gwabi da kuma tallafin karatu.
Tuni dai shugaba Ramaphosa ya bada umarnin gano yadda ake daukar ‘yan kasar zuwa Rasha domin yaki.
Karya doka ne a Afrika ta Kudu dan kasa yaje wata kasa a matsayin sojan haya ko yaki.
Me Ukraine ke cewa?
Ministan harkokin wajen Ukraine yace fiye da ‘yan Afirka 1000 ne suke taya Rasha yaki da kasar Ukraine.
Ministan harkokin wajen Ukraine, Andriy Sabiha, ya ce Rasha tana jawo hankalin matasa daga Afirka ta hanyar kwangilolin da suka yi dai-dai da hukuncin kisa, inda ya bayyana cewa yawancin waɗanda suka shiga aikin sojin Rasha ana tura su kai tsaye cikin yaƙi mai haɗari kuma yawanci suna mutuwa cikin gaggawa saboda rashin cikakkiyar ƙwarewa.
Ukraine ta roƙi gwamnatocin Afirka su gargaɗi ƴan ƙasashensu game da haɗarin shiga wannan rikicin, tana mai cewa Rasha na ƙoƙarin ƙarfafa rundunarta ta hanyar ɗaukar ƴan ƙasashen waje.
