Hukunci: Ƙarya ne
Bisa manyan alamomin da suka tabbatar da hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne, shafin da ya fara wallafa bidiyon da aka ɗakko hoton ya ayyana bidiyon a matsayin haɗin AI, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton na ƙarya ne.
Yayin da ƙasashen duniya da mutane ke cigaba da magana tare da Allah wadai da abubuwan dake faruwa a Sudan.
A duk lokutan wani rikici ko yaƙi hotuna da bidiyon haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI na yaɗuwa domin cimma wata manufa.
Duk da cewa kashe-kashen ko ta’asa na faruwa.
Iƙirari:
Wasu shafukan sada zumunta a Sudan dama waɗanda ke magana da harshen Hausa sun yaɗa wani hotu da ake iƙirarin cewa bayan an ƙona gidan ta ita da yaranta suna jiran mutuwar su.
Wannan shafin Facebook yayi rubutu kamar haka;
“Wata mata ce da Ƴan tawayen Sudan suka jefa a cikin wani kwazazzabo, tana rungume da ɗanta a kirjinta, tana jiran ajalin ta bayan sun ƙone gidanta akan idonta!!
Wannan hoto ba wani shiri ne daga labarin Ashabul Ukhdud ba, wannan hoton daga Sudan ne mai jinya da raɗaɗi, Sudan da aka manta da ita, Sudan da hawaye suka ƙafe, Sudan da duniya bata damu da ita ko ɗan kaɗan ba!!“

Shima wannan shafin facebook ya wallafa wannan hoto tare da dogon rubutu.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta ga no cewa wannan hoto da ake cigaba da yaɗawa haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
A hoton dai akwai alamomi da dama dake tabbatar da hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI misali, inuwar wasu dake tsaye. Sannan shafin Tiktok da shine farko da ya wallafa bidiyon da aka dakko hoton mai suna @khoubaib.bz ya ayyana bidiyon a matsayin haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI.
Alkalanci ta tabbatar da wasu bidiyon kashe-kashe da dakarun RSF sukayi a el-fasher to amma wancan hoto dai ba na gaskiya bane.
Sakamakon bincike:
Bisa manyan alamomin da suka tabbatar da hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne, shafin da ya fara wallafa bidiyon da aka ɗakko hoton ya ayyana bidiyon a matsayin haɗin AI, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton na ƙarya ne.
