Fayyace abubuwaMe yasa ake zargin UAE da Rasha a yaƙin...

Me yasa ake zargin UAE da Rasha a yaƙin Sudan?

-

A wani bidiyo da ya yaɗu matuka anga wani sojan RSF a Sudan yana murmushi yayin wasu ke roƙon da kada a kashe su, to amma sakanni kaɗan aka harbe su.

An bayyana sunan wannan sojan da Abu Lulu.  Bidiyon wannan kisa dai sashen tantance labarai na BBC mai suna BBC Verify sun tabbatar da ingancin sa. Sun kuma bayyana cewa wasu bidiyoyin da dama sun tabbata da cewa dakarun RSF sun kasha fararen hula.

Ta dalilin harin da dakarun RSF suka kai a El-Fasher dake yankin Darfur a ƙasar Sudan ya janyo hankulan duniya kan irin zub da jini da ake yi a ƙasar da yanzu ta rabu gida biyu.

An sha zargin Abu Lulu da kisan gilla ga fararen hula.

Tuni dai shugaban dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya bada umarnin ka ma Abu Lulu wanda yanzu yake fuskantar bincike.

Waɗanne Ƙasashe ake zargi da hannu wajen yaƙin Sudan?

Tunda da aka fara wannan yaƙi dai tsakanin dakarun sojin ƙasar ta Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ake zargin wasu ƙasashe da hannu a ciki.

Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE

Cikin binciken dake alaƙanta UAE da wannan rikici na goyon bayan RSF akwai wanda gidan jarida na Aljazeera yayi dake nuna cewa, akwai sojojin haya daga kasar Colombia sama 300 da wani kamfanin tsaro dake UAE ya ɗauka kuma ya tura zuwa Sudan suna yaƙi tare da dakarun RSF.

Gidan jaridar Sky News cikin hirar sa da wasu manyan dakarun RSF sunce ƙasar ta UAE ce ke ɗaukar nauyin RSF.

Wakilin ƙasar ta UAE a majalisar Dinkin Duniya Mohamed Abushahab ya musanta wannan ikirari na cewa ƙasar sa ce take rura wutar rikicin Sudan ta hanyar goyon bayan RSF.

Ƙasar Rasha

Binciken gidan jaridar Sky News shi kuma ya nuna cewa ƙasar Rasha na da hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikicin ƙasar ta  Sudan, domin an sami sojojin hayar Wagner group suna aiki a kasar a farko-farkon yaƙin.

Kwanakin baya ma dai akwai wani bidiyo da wani babba malamin addini ya sanya a shafin sa wanda aka ga wani jirgi mai saukar ungulu ya sauka a wani fili wasu fararen  fata na sakkowa inda yayi iƙirarin cewa turawa ne ke baiwa ƴan ta’adda makamai.

To sai dai bayan tantance bidiyion Alkalanci ta gano cewa a kasar Sudan ne aka ɗauki wannan bidiyo.

Mai sharhi da kawo rahoton tsaro mai suna Zagazola Makama ya bincike bidiyon inda ya gano cewa jirgin ƙirar kasar Rashe ne kuma fararen fatar ma turawan Rasha ne.

Binciken ƙasa da ƙasa dai ya sha bankaɗo tare da nuna yadda sojojin hayar na Rasha a ƙasashen Afirka da aikata kisan gilla da take haƙƙin bil’adama.

A kwanakin baya ma dai wani binciken gidan jaridar Daily Trust ya nuna cewa akwai gwal ɗin Zamfara na zuwa Dubai na ƙasar ta UAE.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar