Tun shekarar 2021 dai Janar Assimi Goita ke mulkin ƙasar Mali bayan ya aiwatar da juyin mulki.
Cikin abinda shugabannin juyin mulkin suka bayyana na dalilin yinsa shine matsalar tsaro.
Bayan juyin mulkin nasa dai an ɗan sami raguwar matsalolin tsaro na wucin gadi to amma daga baya abubuwa suka cigaba da ta’azzara.
Mali dai ta fice daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS tare da ƙasashen Burkina Faso da Nijar, sun dai haɗa ƙungiyar AES tare da shan alwashin haɗa kai domin kawo tsaro a yankin.
Ƙasashen ukun dai na fama da hare-haren ƙungiyoyin ta’addanci wanda har zuwa shekarar 2025 ana samun munanan hare-hare wanda rahoton tsaro na kungiyoyin ƙasa da ƙasa suka bayyana cewa ayyukan ta’addanci ƙaruwa yayi a waɗannan ƙasashe.
Meke Faruwa a Mali?
Tun daga 4 ga watan Satumba, 2025 ne dai ƙungiyar ta’addanci ta JNIM ta rufe hanyoyin shigar da mai zuwa gurare da dama na ƙasar wanda ya haɗa da babban birnin ƙasar.
Rashin man fetur ɗin dai shine ya tilasta kamfanin haƙar gwal na ƙasar ta Mali mai suna Sadiola ya tsayar da aiki cak a 4 ga watan Oktoba na wannan shekarar. Ayyukan kamfanin dai sune ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasar a yanzu.
A ranar 23 ga watan Oktoba ne dai ƙungiyar ta’addanci ta JNIM ta ayyana babu shigar da mai Mali wanda ya janyo gwamnatin ƙasar sanar da hutun makarantu da jami’o’i saboda ƙarancin man fetur.

Farashin litar man fetur ta kai Sefa dubu huɗu (4,000 CFA) ga kuma ƙarancin man wanda ya tilasta aka sanya sojoji gadin gidajen man fetur a babban birnin ƙasar.
A yanzu dai ƙungiyar ta JNIM itace ke jagorancin ɓangarorin ƙasar, wanda hana shigo da man fetur din ya nuna ƙarara yadda ƙarfin ƙungiyar take a ƙasar duk da shan alwashin da shugaba Assimi yayi na kawo zaman lafiya ga ƴan ƙasar.
Ƙungiyar Ƴan jaridu ta Reporters without borders ta ayyana Mali a matsayin ƙasar data fi kowacce hatsari ga ƴan jaridu a yankin Sahel saboda yadda ake kamasu da kuma tura su gidan yari.
Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin Janar Assimi Goita dai ta ɗaure mutane da dama wanda ya haɗa da sojojin da sukayi juyin mulkin tare, masu fafutuka da sauran su.
Sulhu
A watan Janairun shekarar 2024 ne dai gwamnatin Mali ta soke yarjejeniyar dake tsakaninta da ƙungiyoyin dake ɗauke da makamai wanda ƙasar tayi a shekarar 2015.
Gwamnatin ƙasar ta Mali dai na neman wanda zai shiga tsakanin gwamnatin da ƙungiyar JNIM domin kawo ƙarshen ƙarancin man fetur. Wannan yinƙuri dai masu sharhi na ganin alamu ne na kasawa.
Sojin Rasha
Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar tarayya Afrika AU sun gargaɗi ƙasashe su guji ɗakko sojojin haya.
To amma a shekarar 2021 gwamnatin sojin Mali ta gayyaci sojojin hayar ƙasar Rasha mai suna Wagner Group. Tun bayan zuwan Wagner dai an sami kisan fararen hula, take hakkin bil’adama tare da kwashe makaman yaƙin sojin ƙasar ta Mali.
A tsakanin 2021 zuwa 2025 dai akwai aƙalla sojojin haya daga Rasha da suka kusan 2,000 a ɓangarorin ƙasar daban-daban.
Duk da cewa babu cikakken bayanin nawa gwamnatin Mali ke kashewa wajen biya sojin hayar, amma hukumomin Amurka sun yi iƙirarin cewa ana biya Wagner Group Dala miliyan goma a wata ($10 million).
A watan Mayun wannan shekarar ta 2025 Wagner ta ayyana janyewa daga Mali to amma reshen ma’aikatar tsaron Rasha mai suna Africa Corps ta maye gurbin ta.
To amma kashi 75 zuwa 80 na sojojin Africa Corps daga Wagner Group suke a cewar rahoton Global initiative against transnational organized crime.
