Akwai wani bidiyo dake yaɗuwa matuka a kafafen sada zumunta, inda ake nuna cewa ɓera ya firgita mai gabatar da labarai a ɗakin watsa labarai na gidan Talabijin na Aljazeera.
Iƙirari:
Wani shafin facebook mai suna Abdulmumin Abubakar Tsanyawa ya wallafa bidiyon inda ya rubuta; “ Bera cikin studion Aljazira ”
Wannan bidiyo dai ya yaɗu matuka a gurare da dama kamar nan.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa gidan jarida na newsbuzz247 ya tantance wannan bidiyo tare da yanke hukuncin cewa haɗin AI ne.
Haka zalika wata kafar jarida dake aikin tantance labarai a ƙasar indiya mai suna LatestLY itama ta tantance wannan labara tare da yanke hukuncin cewa haɗin AI ne.
Duk da wannan bayanai Alkalanci ta kalli bidiyon da kyau inda akwai gurare dake nuna cewa bidiyon haɗashi akayi. Na farko muryar alamun anyi amfani da AI akanta, haka zalika bayan da mai gabatarwar ta tashi tsaye kujerar ta juya baya amma sai aka ga ta dawo ta zauna ba tare da ta juyo da kujerar ba. Sannan tsayar da bidiyon domin duba beran ya nuna cewa ba kamar yadda idan beran gaskiya bane.
Sakamakon bincike:
La’akari da cewa wasu kafafen tantance labarai sun tabbatar da bidiyon na AI ne, tare da irin lurar da Alkalanci tayi na yadda ta zauna ba tare da ta juyo da kurar ba, da kuma yanayin sautin muryar ya tabbatar da cewa bidiyon hadin AI ne.
